A gobe 5 ga wata da safe a nan birnin Beijing, za a kira taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wadda ta kasance hukumar koli ta kasar Sin. Taron kuma zai zama na farko na sabuwar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin.
Bisa labarin da wakilinmu ya samo a yau 4 ga wata daga wajen taron share fage da kuma taron tawagar shugabanni da aka gudanar, an ce, gaba daya wakilan jama'a 2987 ne ke cikin sabuwar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kuma yanzu akwai 2982 da suka yi rajistar isowa nan birnin Beijing. A cikin kwanaki 13 da rabi da za a yi ana taron, wakilan za su yi nazari a kan rahotannin aiki da gwamnati da zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da kotun kolin jama'ar kasar Sin da kuma kotun kolin binciken shari'a na jama'ar kasar Sin suka gabatar. Sa'an nan, za su kuma duba shirin gyaran tsarin hukumomin majalisar gudanarwa ta kasar Sin, da zaben sabon shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da mataimakin shugabansa da babban sakatarensa da kuma wakilansa, tare kuma da zaben shugaban kasar Sin da kuma mataimakin shugaban kasar. Bayan haka, za a kuma tabbatar da wanda za a nada shi don ya zama firaministan kasar Sin da kuma wanda zai zama mataimakin firaminista da ministoci da dai sauran muhimman mukamai a cikin majalisar gudanarwa ta kasar Sin. Ban da wadannan, a gun taron, za a kuma zabi shugaban kwamitin tsakiya na sojan kasar Sin da kuma tabbatar da wanda zai zama mataimakin shugabansa da wakilansa, a yayin da za a kuma zabi shugaban kotun kolin jama'ar kasar Sin da shugaban kotun koli na binciken shari'a ta jama'ar kasar Sin.
A lokacin taron kuma, za a gudanar da tarurrukan manema labarai da dama, inda za a gayyaci manyan jami'an sassan majalisar gudanarwa ta kasar Sin, domin su amsa tambayoyin manema labarai da ke shafar manufar Sin kan kasashen waje da bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma da ba da jagoranci daga manyan fannoni da muhalli da albarkatun kasa da tsimin makamashi da rage fitar da sinadarai masu gurbata muhalli da sauransu. Bayan da aka rufe taron a ranar 18 ga wata, firaministan kasar Sin zai gana da manema labarai na gida da na waje, don amsa tambayoyin da ke daukar hankulansu.(Lubabatu)
|