Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-04 16:14:13    
Kallon tsuntsaye a tsibirin tsuntsaye a tabkin Qinghaihu

cri

Masu sauraro, barkanku da war haka, yanzu lokaci ya yi da muka fara shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin. Ni ce Tasallah da mu kan sadu a ko wace ranar Talata. A lardin Qinghai da ke arewa maso yammacin kasar Sin, mashahurin tabkin Qinghaihu ya yi kama da lu'ulu'u, an hada shi a cikin filin ciyayi maras iyaka. Tsibirin tsuntsaye a wannan tabki ya zama shahararren wurin yawon shakatawa saboda dubban tsuntsaye masu yin hijira su kan zama a wurin a ko wace shekara. Yau ma bari mu shiga wannan wuri da 'yan Adam da tsuntsaye suke zama tare.Tsibirin tsuntsaye na cikin kusurwa ta arewa maso yammacin tabkin Qinghaihu, an raba shi zuwa kashe 2, wato na gabas da na yamma. Mutane suna iya jin kukan tsuntsaye iri daban daban daga nesa. In an isa wurin kallo, ana iya ganin tsuntsaye iri daban daban suna wasa a tsakanin sararin sama da ruwan tabkin, wasu suna tafiya sun ratsa sararin sama, wasu suna kuma wasa da juna, sun fito da igiyar ruwa a fuskar ruwan tabkin, wasu kuwa suna kwance a karkashin hasken rana a bankin tabkin.

Saboda isowar dimbin tsuntsaye masu yin hijira, sannu a hankali tsibirin tsutsaye a tabkin Qinghaihu ya zama shahararren wurin yawon shakatawa. Masu yawon shakatawa da yawa na gida da kuma na ketare suna bin sawun tsuntsaye masu yin hijira, sun zo nan domin kallon dubban tsuntsaye a lokaci guda. Bisa kididdigar da aka yi, tun bayan shekarar 2003 har zuwa yanzu, matsakacin yawan wadanda suka kawo wa tsibirin tsuntsayen ziyara ya kai kimanin dubu 100 a ko wace shekara.

A cikin wadannan masu yawon shakatawa da suke son more idonsu da kyawawan tsuntsaye, Li Shehui, wanda ya zo daga birnin Xi'an na arewa maso yammacin kasar Sin ya gaya mana cewa, shi da matarsa da kuma 'yarsa sun kawo wa tabkin Qinghaihu ziyara tare a wannan karo. 'Yarsa ta dade tana zama a cikin birni, shi ya sa ta ji farin ciki kwarai saboda ganin tsuntsaye masu yawan hakan a karo na farko. Li ya ce, 'Na zo tsibirin tsuntsaye tare da diyata domin kallon tsuntsaye. Na gaya mata cewa, tsuntsaye sun dade suna zama a wurin, suna da nasaba da 'yan Adam sosai. In mutane za su iya kiyaye muhalli kamar yadda ya kamata, to, tsuntsaye za su sami kyakkyawar kiyayewa.'

Lalle, kamar yadda malam Li ya fada, tsuntsaye suna da nasaba da 'yan Adam sosai. A matsayinsa na muhimmin bangare na tudun Qingzang, tabkin Qinghaihu na matsayin wurin da ya kan sami tasiri ko kuma illa a sakamakon sauye-sauyen yanayi cikin sauki, haka kuma, tsarin muhallin halittu ba ya da inganci sosai ba. Shi ya sa tilas ne a fi mai da hankali kan kiyaye muhalli in aka nemi raya aikin yawon shakatawa a wurin. Xu Hao, mataimakin shugaban hukumar aikin yawon shakatawa ta lardin Qinghai ya bayyana cewa, ko kusa ba su yarda da raya aikin yawon shakatawa tare da sadaukar da gurbata muhalli ba. Ya ce, 'A ganinmu, tilas ne mu dogara da kyakkyawan muhallin halittu wajen raya aikin yawon shakatawa na muhalli. Tabkin Qinghaihu wani kyakkyawan wurin yawon shakatawa ne mai sigar musamman. Ko kusa ba za mu yarda da ganin ya bace ko kuma an lalata shi ba. Kazalika kuma, in aka lalata tabkin, to, ba za a iya kiyasta illolin da za a kawo ba, ta haka mai yiwuwa ne mutane za su gamu da matsala a zaman rayuwarsu, balle ma raya aikin yawon shakatawa.'

Don hana aikace-aikacen mutane su kawo ga tsuntsayen da ke zama a tabkin Qinghaihu illa a fannin muhallin rayuwa, hukumar kula da shiyyar kiyaye halitta ta tabkin Qinghaihu ta tsara jerin matakai. He Yubang, mataimakin shugaban hukumar ya gaya mana cewa, 'Kada mutane su kusanci tsuntsaye. Wanzar da jituwa a tsakanin 'yan Adam da tsuntsaye bai nuna cewa, dole ne mutane su yi zama tare da tsuntsaye kafada da kafada ba. A'a, ba haka ba ne, wannan zai fi damun tsuntsaye.'

Don yin iyakacin kokari wajen hana damun tsuntsayen da suka yi hayayyafa, a wuraren da aka samu dimbin kwayayen tsuntsaye, an gina wani dakin da rabinsa yake cikin karkashin kasa, inda masu yawon shakatawa suna iya kallon tsuntsaye ta ramukan kallo. An shafa wannan daki da ciyayi. In ba a mai da hankali sosai ba, to, da kyar a bambanta shi da abubuwan da ke kewayensa ba. Ta haka, mutane na iya ganin tsuntsaye, amma tsuntsayen ba su iya ganin mutane ba.

Ko da yake masu yawon shakatawa ba su saba wa irin wannan hanyar kallon tsuntsaye ba, amma yawancinsu sun nuna fahimta da kuma goyon baya.

A idon wasu, tabkin Qinghaihu yana kan matsayin farko a lardin Qinghai wajen raya aikin yawon shakatawa, haka kuma, tsibirin tsuntsaye a tabkin ya yi kamar lu'ulu'u a cikin wannan kambi. Yanzu tsibirin ya zama wurin yawon shakatawa na kallon tsuntsaye, haka kuma yana matsayin aljanna ga tsuntsaye da su yi zama da kuma yin hayayyafa. Ana daukar matakai domin kiyaye tabkin Qinghaihu, ta haka tsibirin tsuntsaye zai zama wurin da tsuntsaye da 'yan Adam suke zama tare cikin jituwa.