Saurari
Ran 3 ga wata da yamma, mambobi fiye da dubu 2 na kwamitin harkokin kasar Sin na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin da suka fito daga wurare daban daban na kasar sun halarci farkon taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin a karo na 11. Wadannan mambobi sun halarci wannan taro na farko a wannan shekara tare da burin al'ummar kasar Sin na rukunoni daban daban.
Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, muhimmiyar hukuma ce da ke karkashin shugabancin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma jam'iyyu suke hada gwiwa a tsakaninsu, suke ba da shawara kan harkokin siyasa. Ta hada da kwamitin duk kasar da kwamitocin harkokin kananan hukumomi. Bisa ka'idojin da aka tsara, a kan zabi sabbin mambobin majalisar sau daya a ko wadanne shekaru 5. A shekarar bana, za a zabi sabbin mambobin wannan kwamiti. Shi ya sa taron da aka fara yi a yau, taron shekara-shekara ne da sabon kwamitin harkokin kasar ya yi a karo na farko a wannan shekara. Shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da na gwamnatin kasar sun halarci taron.
Jia Qinglin, shugaban zaunannen kwamitin duk kasar na majalisar ya ba da rahoton aiki a madadin mambobin zaunannen kwamitin harkokin kasar na karo na 10, inda ya ce,'A cikin shekaru 5 da suka wuce, mun ba da dimbin muhimman shawarwari kan tsarawa da aiwatar da shirin raya kasa na tsawon shekaru 5 da raya zaman al'ummar kasa na gurguzu mai jituwa da ingantawa da kyautata raya tattalin arziki daga manyan fannoni da bunkasa sabon kauye na gurguzu da raya kasa ta kirkire-kirkire da raya zaman al'ummar kasa, wadda ke dora muhimmanci kan yin tsimin makamashi da kiyaye muhalli da kuma kyautata tsarin tattalin arziki da canza hanyoyin bunkasuwa da sauran muhimman batutuwa.'
A cikin rahotonsa, Jia ya bayyana cewa, a cikin shekaru 5 da suka wuce, zaunannen kwamitin harkokin kasar na karo na 10 ya karbi shawarwari fiye da dubu 23, a ciki kuma wasu fiye da dubu 6 da dari 6 sun bayyana nufin al'umma da kuma zaman al'ummar kasa.
Hukumomin gwamnatin sun shigar da da yawa daga cikin wadannan shawarwari domin tsara manufofi. Wang Xi, wani mamban kwamitin harkokin kasar ya nuna ra'ayinsa game da wannan fanni. Shawararsa game da yin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli ya janyo hankalin kwamitin yin gyare-gyare da raya kasar Sin, gwamnatin kuma ta tanade ta cikin manufa. Ya ce,'A shekarun baya, kasar Sin ta sami babban ci gaba a kan yin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli. Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta kaddamar da jerin takardun musamman a wannan fanni, ta kuma tsara makasudi filla-filla. Yanzu kananan hukumomin kasar suna himmantuwa wajen aiwatar da wadannan makasudi. A galibi dai kasar Sin tana cikin hali mai kyau wajen tabbatar da wannan makasudi.'
1 2
|