Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-03 16:22:59    
Yanzu kuma za mu kawo muku wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Bisa sabon kididdigar da aka yi an ce, tun bayan da aka fara aikin jigilar gas daga yammacin kasar Sin wato daga filin hakar man fetur na Talimu na jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar zuwa gabashin kasar, yawan iskar gas da aka yi jigilarsa zuwa gabashin kasar ya wuce kubic mita biliyan 30, sabo da haka jihar Xinjiang ta riga ta zama jiha mafi girma ta kasar Sin wajen fitar da iskar gas zuwa sauran wurare.

Domin sayar da iskar gas mai albarka ta jihar Xinjiang zuwa kasuwannin gabashin kasar Sin, daga shekarar 2002 kasar Sin ta fara shimfida bututun jigilar gas daga yammacin kasar zuwa gabashin kasar, daga shekarar 2004 kuma ta fara tafiyar da wannan aiki bisa hanyar kasuwanci. Bisa karfin ingizawa na wannan aikin jigilar gas daga yammacin kasar Sin zuwa gabashin kasar, yawan iskar gas da aka fitar daga jihar Xinjiang ya karu da sauri, yawan iskar gas da ake jigilarsa zuwa sauran wurare shi ma yana ta karuwa.

Yawan iskar gas da jihar Xinjiang take jigilar a kowace rana ta hanyar bututun gas ya wuce kubic mita miliyan 40, ta yadda aka tabbatar da aikin samar da gas ga mutane fiye da miliyan 200 cikin zamansu na yau da kullum.

---- Kwanan baya wakilinmu ya samu labari daga hukumar sufuri ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin cewa, cikin shekarar da muke ciki jihar Tibet za ta ware kudin sin wato Yuan biliyan 6 domin shimfida hanyoyin mota, ta yadda za a yi kokarin cimma manufar kashi 99 bisa 100 na dukkan gundumomi da garuruwan jihar su samu hanyoyin mota.

Yanzu jimlar tsawon hanyoyin mota da aka shimfida a jihar Tibet ta kai kilomita dubu 44.8, an kimanta cewa, zuwa shekarar 2010, wannan adadi zai karu har ya kai kilomita dubu 50, mamoma da makiyaya na jihar Tibet za su kara samun kudin shiga da yawa ta hanyar shimfida hanyoyin mota, sa'an nan kuma za su iya jigilar amfanin gona da na dabbobi zuwa sauran waurare ta hanyar mota. Ban da wannan kuma bisa ci gaban da ake ta samu a kowace rana wajen sufurin hanyoyin mota, manoma da makiyaya na jihar Tibet za su kara samun kudin shiga da yawa ta sana'a yawon shakatawa.

---- Yayin da ake ci gaba da yin bikin sabuwar shekara ce bisa kalandar kabilar Tibet, mutane masu yawan gaske sun kai ziyara birnin Lhasa, hedkwatar jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin don yin addu'a.

An ce, a gun bikin sabuwar shekara bisa kalandar kabilar Tibet, yanayin addini ya game ko'ina a birnin Lhasa. Sabo da hanyar dogo da aka shimfida ba da dadewa ba ta kawo sauki ga masu bin addinin lardin Qinghai da na Gansu da su shiga jihar Tibet don yin addu'a, shi ya sa cikin shekaru 2 da suka wuce, yawan masu bin addini da suka je wurin ibadan Jokhan don yin addu'a ya karu sosai. Tun daga jajibirin sabuwar shekara zuwa yanzu, kullum ana yin jerin gwano a bakin kofar ibadan Jokhan domin jiran yin addu'a, masu bin addini sun shiga cikin babban dakin ibadan, sun kewaya mutum-mutumin budda, sun zuba man shanu cikin fitilu, da ba da kyautar farin kyallen da ake kira Hada, kuma sun dauki alwashi a gaban budda don nuna biyayya ga addini da bayyana kyakkyawan fata ga zaman rayuwarsu.