Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-03 15:59:23    
An bude taron shekara shekara na sabuwar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin a karo na farko a birnin Beijing

cri

A ran 3 ga wata da yamma, an bude taro na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa a karon na 11 na kasar Sin a birnin Beijing.

Abu mai muhimmanci da za a yi a taron nan shi ne wakilai sama da dubu 2 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa za su saurara da kuma dudduba rahoton ayyukan zaunanen kwamitin majalisar ba da shawara da shugaban majalisar ba da shawara Mr. Jia Qinglin ya bayar.

An canja membobin majalisar ba da shawara na kasar Sin a ko wace shekara biyar, taron nan da za a shafe kwanaki 11 ana yinsa ya zama taron shekara shekara na farko da sabuwar majalisar ba da shawara ta shirya. Shugabannin jam'iyyar kuma shugaban kasa Hu Jintao, da Wu Bangguo, da Wen Jiabao, da Jia Qinglin sun halarci bikin bude taron. (Zubairu)