Ran 2 ga wata da yamma a nan birnin Beijing, an bude taron shirya taro na farko na kwamiti na karo na 11 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na jama'ar kasar Sin.
Membobi 2103 daga wurare dabam daban na wannan kwamiti sun halarci wannan taro, kuma sun zartar da sunayen kungiyar manyan membobi, da jagora da babban sakatare na wannan kungiya, da ajandu, da lokacin da za a yi tataunawa, da sunayen membobin kwamitin binciken shawara.
Bisa ajandu, za a bude taro na farko na kwamiti na 11 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa tun ran 3 ga wannan wata. Mr. Jia Qinglin memban zaunanen kwamiti na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban majalisar na 10 zai yi bayani kan aikin zaunanen kwamiti na majalisar.
A ran 5 ga wata, dukkan membobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa za su halartar taron majalisar wakilan jama'a na karo na 11, da kuma saurari bayanin da firaminista Wen Jiabao zai yi kan aikin gwamnati.
|