Ran 2 ga wata da safe, masu halartar taron majalisar wakilan jama'a daga lardin Hu'nan da ke tsakiyar kasar Sin sun sauka nan birnin Beijing, za su halartar taro na karo na farko na majalisar wakilan jama'a ta zagaye na 11 da za a gudanar da shi daga ran 5 ga wannan wata.
A wannan rana kuma, bi da bi ne kungiyoyin wakilan da suka zo daga lardunan Heilongjiang, da Hubei, da Jiangsu, da Hu'nan, da Jilin, da Anhui sun sauka birnin Beijing.
Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ita ce hukumar ikon koli ta kasar Sin, tana gudanar da ikon kafa dokoki, da yanke hukunci kan manyan harkokin siyasa. Wakilai na wannan majalisar suna da wa'adi na shekaru 5 na ko wane zagaye. Majalisar wakilan jama'a na zagaye na 11 tana kunshe da wakilai 2987. shugabanni Hu Jintao, da Wu Bangguo, da Wen Jiabao sun zama wakilai daga hukumomi dabam daban.
Ban da haka kuma, za a gudanar da taron shekara shekara na wata muhimmiyar hukuma daban da jam'iyyar kwaminista ta kasar Sin ke yi mata jagora, wato majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar. Yanzu, bi da bi membobin majalisar fiye da 2200 suke yin rajistan sunayensu.
|