Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-29 16:40:13    
Bangaren kasar Sin ya dora muhimmanci sosai a kan dangantakar da ke tsakanin Sin da Nijeriya, in ji malam Wu Bangguo

cri

Ran 29 ga wata, a nan birnin Beijing, yayin da shugaban zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin Mr. Wu Bangguo ya gana da shugaban kasar Nijeriya Umaru Musa 'yar Adua, ya bayyana cewa, bangaren kasar Sin ya dora muhimmanci sosai a kan dangantakar da ke tsakanin Sin da Nijeriya, yana fatan za a kara zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu.


Wu Bangguo ya bayyana cewa, tun lokacin da Sin da Nijeriya suka kafa huldar diplomasiyya tsakaninsu, an gudanar da dangantaka ta bangarori biyu lami lafiya kuma cikin armashi, an sami sakamako mai kyau wajen yin hadin gwiwa na kawo moriyar juna daga dukkan fannoni da ke tsakaninsu. Hadin gwiwa tsakanin hukumomin shari'a na kasashen nan biyu ya zama muhimmin kashi da ke tsakaninsu. Majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin ta dora muhimmanci sosai wajen bunkasuwar dangantaka tare da majalisar dokoki ta Nijeriya, tana son ci gaba da yin mu'ammala cikin aminci, don ingiza dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakaninsu.


Alhaji 'yar Adua ya bayyana cewa, bangaren kasar Nijeriya yana son kara yalwata hadin gwiwa tare da kasar Sin wajen samar da wutar lantarki, da albarkatun kasar, da manyan ayyuka da sauran muhimman fannonin bunkasuwa na kasar Nijeriya, da inganta mu'ammala tsakanin jam'iyyun siyasa biyu da majalisun dokokin kasar, don zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Nijeriya da Sin daga dukkan fannoni.(Bako)