Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-29 10:14:06    
Kasar Sin da Nijeriya sun ba da hadaddiyar sanarwa

cri

Ran 28 ga wata, a nan birnin Beijing, kasar Sin da Nijeriya sun ba da hadaddiyar sanarwa.

A cikin sanarwar, an bayyana cewa, bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi masa, ran 27 ga watan Febrairu zuwa ran 1 ga watan Maris na shekarar 2008, shugaban jamhuriyar tarayyar Nijeriya, Alhaji Umaru Musa 'yar Adua ya kawo wa kasar Sin ziyarar aiki. A lokacin ziyararsa, shugabannin kasashen nan biyu sun waiwayi kyakkyawar dangantaka ta bangarorin biyu wato tsakanin Sin da Nijeriya bayan da aka kafa huldar diplomasiyya tsakaninsu, kuma bangarorin biyu sun yanke shawara cewa za su inganta shawarwarin siyasa tsakaninsu, kuma za su kaddamar da yin shawarwari a daidaitaccen lokaci kuma bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu, don ci gaba da zurfafa dangantakar da ke tsakanin Sin da Nijeriya, da kuma inganta hadin gwiwa bisa moriyar juna wajen tattalin arziki da hadin gwiwa tsakaninsu.

Bangaren kasar Sin ya yaba wa kasar Nijeriya kan muhimmiyar rawa da ta taka wajen sha'anin kiyaye zaman lafiya a Afrika a tsawon lokaci, bangaren kasar Nijeriya ya yaba gudumawar da kasar Sin ta yi wajen nuna goyon baya ga kungiyar AU da ta warware rikice-rikice a Afrika cikin ruwan sanyi. Kusoshi na kasashen nan biyu sun yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su kara samar da goyon baya don ciyar da aikin jibge sojojin hadin gwiwa na kungiyar AU da M.D.D a yankin Darfur gaba tun da wurwuri.(Bako)