Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-28 18:35:42    
Sin na ganin cewa Jiaozi mai dafi da ta fitar zuwa Japan batu ne da ya shafi mutum guda kawai

cri
Yau ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta Sin ya kira taron manema labarai kan cin guba cikin Jiaozi, wato wani irin abincin Sinawa, wanda Sin ta fitar zuwa Japan. A gun taron, 'yan sandan kasar Sin da jami'in da abin ya shafa na babbar hukumar sa ido kan ingancin kayayyaki da binciken cututtuka ta kasar Sin sun sanar da sakamakon binciken da suka gudanar kan al'amarin. A ganin bangaren Sin, batun na shafar mutum guda ne kawai a maimakon batun ingancin abinci da ragowar maganin kwari ya haddasa, kuma mawuyaci ne a ce an sanya dafi a kasar Sin.

A karshen watan Janairu da ya wuce, ma'aikatar kula da harkokin kiwon lafiya da kwadago da jin dadin jama'a ta kasar Japan ta sanar da babbar hukumar sa ido kan ingancin kayayyaki da binciken cututtuka ta kasar Sin cewa, wani dan kasar Japan ya ci guba cikin Jiaozi da Sin ta fitar zuwa Japan, har ma ya fara amai, bayan da aka kai shi asibiti kuma, an gano sinadarin methamidopho, wato wani irin maganin kwari a cikin amansa, tare kuma da jakar leda da ta dauki abincin. Daga baya, 'yan sandan Japan sun yi bincike a kan irin wannan Jiaozi da ake sayawar a kasuwannin Japan, amma ba a gano gubar methamidopho ba. Bayan da ta sami sanarwar, gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci sosai a kan al'amarin, kuma sassan da abin ya shafa sun dauki matakai cikin sauri. Babbar hukumar sa ido kan ingancin kayayyaki da binciken cututtuka ta kasar Sin ta gudanar da bincike a kan samfurin da aka dauko daga Japan tare kuma da masana'antar Tianyang da ke lardin Hebei na kasar Sin wadda ita ce ta yi abincin, a yayin da ma'aikatar tsaron lafiyar jama'a ta kasar Sin ta tura kungiyar ma'aikatanta zuwa lardin Hebei don yin bincike a kan danyun kayayyaki da masana'antar ke amfani da su da kuma yadda take yin abincin da kuma jigilarsu. Mr.Yu Xinmin, wani jami'in ma'aikatar tsaron lafiyar jama'a ta kasar Sin wanda ke kula da binciken ya ce,"sakamakon binciken ya tabbatar da cewa, masana'antar abinci ta Tianyang na gudanar da harkokinta sosai, da kyar a kai gubar methamidopho a cikin dakin aikinta, kuma ma'aikatanta na gudanar da aiki ne tare, wato suna sa ido a kan juna, sa'an nan an sa camera, wato na'urorin daukan hoto a cikin dakin aikinta, shi ya sa da wuya a sami damar sa dafi. Bayan haka, an sa jiaozi da za a fitar zuwa kasashen waje cikin akwatuna nan da nan bayan da aka yi shi, sa'an nan an yi jigilarsu zuwa Japan, a yayin da bangaren Japan ya bude su, bai gano abin da bai kamata ba. Sabo da haka, 'yan sandan kasar Sin na ganin cewa, batun al'amarin musamman ne da ya shafa mutum guda ne kawai a maimakon batun ingancin abinci. Kuma bisa cikakken binciken da aka yi tare kuma da gwajin da aka gudanar, muna ganin cewa, mawuyaci ne a sanya guba a kasar Sin."

Sakamakon aukuwar al'amarin, kwanan nan, masaya na Japan sun fara damuwa da ingancin abincin kasar Sin. Mr.Wei Chuanzhong, mataimakin shugaban hukumar kula da ingancin abinci da binciken cututtuka ta kasar Sin ya bayyana cewa, a shekarar bara, yawan abincin da Sin ta fitar zuwa Japan wadanda suka cancanta a yi amfani da shi ya kai kashi 99.81%, kuma adadin ya fi na abincin da Japan ke fitarwa zuwa kasar Sin kadan. A cewar Mr.Wei Chuanzhong, ba ma kawai gwamnatin kasar Sin ke daukar nauyin ingancin abinci jama'arta, haka kuma tana daukar nauyin lafiyar dukan masayan abincin kasar Sin." Ya ce,"ingancin abinci matsala daya ce da ke gaban kasashe daban daban gaba daya, kuma ana fatan Sin da Japan za su iya gaggauta kafa tsarin hadin gwiwa kan ingancin abinci, don inganta hadin kan kasashen biyu a fannin ingancin abinci da kuma sa kaimi ga bunkasuwar cinikin da ke tsakaninsu yadda ya kamata."