Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-28 14:27:42    
Zaman wani saurarin Indiya a kasar Sin

cri

Sunan saurayin nan shi ne Chaudhari Dillip Giridhar. Yana kaunar birnin Taiyuan na lardin Shanxi dake tsakiyar kasar Sin sosai. yana koyar da turanci a wata jami'a a shekarun baya, yana kuma koyon wasan Gongfu na kasar Sin, ya kasance mai kishin wasan Gongfu na kasar Sin sosai. ya ce,

"Ina da wani sunan daban na kasar Sin wato Chen Ailong, domin Long yana wakiltar al'adu da fasahar kasar Sin. Long yana nufin Mr Bruce Li ne da na ke bauta. Ina kaunar al'adun Sin ina kaunar Bruce Li kuma ina kaunar kasar Sin, shi ya sa na sami wannan suna Ailong."

Kamar baki masu tarin yawa su ke, Mr Chen Ailong ya fara kaunar al'adun kasar Sin ne sabo da ya yi kallon siniman kasar Sin. Wata rana da dare, wannan saurayi maras karfi kuma mai kawaici Chen Ailong ya samu damar kallon wani film da shahararren dan wasa Bruce Li ya taka muhimmiyar rawa a ciki, Bruce Li ya girgiza zuciyarsa sabo da halin rashin tsoron kome da ya nuna yayin da ya ke tsayawa kan adalci, da kuma ayyukan da ya yi na rashin misali cikin sinima.Ya ce,

" Ina so in karo ilimi na game da al'adun kasar Sin da ainihin wasannin Gongfu, ina mafarkin zuwa kasar Sin wata rana. Zuwan kasar Sin ya zama mafarkina, ina so in ga kasar Sin da idona da zama a cikinta."

Mafarkin Cheng Ailong ya cika a shekara ta 2002 sabo da ya samu wata takardar gayyata da jami'ar horar da malaman koyarwa ta lardin Shanxi ta aika masa. A kan matsayin malamin koyarwa na Turanci a baka ya zo nan kasar Sin. Yayin da ya sauka a filin jiragen sama na duniya na hedkwata a nan birnin Beijing, ya yi mamaki sosai kan abin da ya gani da abin da ya yi tsammani a da sabo da karancin ilimin da ya ke da shi kan tarihin Sin da al'adunta. Ya ce,

" Da na sa kafa a yankin kasar Sin bayan da na bar kasar Indiya a karo na farko, ina jiran kallon gine gine na gargajiya da tufaffi na al'ada da ake sawa, amma abun farko da na gani ya sha bamban da abin da na samu daga filafilai kwarai da gaske. Wani babban birni na zamani ya bullo a gabana. Abin da na yi tsammani ya zama abin ban dariya."

Da saukarsa ke da wuya a kasar Sin,Chen Ailong bai saba da zaman kasar Sin ba. A mako na farko da ya fara zamansa a kasar Sin, ya yi fama da rashin lafiya. Sa'ad da yake tunanin tashin daga aikinsa, sai aminan kasar Sin sun nuna masa aminci ta hanyoyi dabam daban, sun taimake shi yayin da ya ke bukata, wannan ya karfafa zuciyarsa sosai. domin sajewa kansa da mutanen Sin, Ailong ya fara koyon harshen Sinanci, ya yi kokarin yin mu'amala da abokai masu aiki rare da shi, ya kara iliminsa game da kasar Sin.

Domin cika burinsa na farko, Ailong ya yi kokarin koyon fasahar kasar Sin cikin yin amfani da zarafin da yake iya samu. Ya yi yawon bude ido a birane da dama na kasar Sin. Ya tafi dakin ibada na Shaolin a tudun Songshan dake lardin Henan,wurin da ya fi shahara kan wasannin Gongfu Shaolin, ya yi koyi da wasannin Shalin, ya kuma je Nanchang na lardin Jiangxi ya yi koyi da wasannin motsa jiki na gargajiya na Taiji na kasar Sin. A cikin kokarinsa na koyon wasannin gargajiya na kasar Sin ya gano makomarsa da kuma abu mafi muhimmanci na wasannin motsa jiki na gargajiya na kasar Sin. Ya ce,

"koyon wasannin Gongfu ya sa na sami nitsuwa a zuciya. Na koyi da wasannin Gongfu ne ba domin cimma nasara kan saura ba,a'a ina so in kare daukacin mutanen da na ke so, wasan Gongfu ya ba ka kuzari da himma da kuma karfi da kuma hazikanci, a ganina wannan abu ne mai muhimmanci a wasan Gongfu, ina mai ra'ayin cewa wannan halaye ne na mutanen kasar Sin."

Mr Chen Ailong yana din dadin zama da aiki a kasar Sin cikin shekarun baya. Yayin da gidan talabiji na birnin Beijing ya shirya wata gasar gwada kwarewar baki kan fasahohin kasar Sin a shekara ta 2006, Chen Ailong ya shiga wani wasan nishadi na shirye shiryen gidan talabiji a karo na farko, inda ya yi wasan motsa jiki na gargajiya na kasar Sin har ya sami kyautar yabo ta matsayi na uku. Daga nan Chen Ailong ya shiga shirye shiryen wasannin gidajen talabiji na kasar Sin. 'yan kallo na kasar Sin sun gano gwanintarsa a fannin wasanni. Ya kayatar da mutanen Sin da wakoki da raye raye na gargajiya da wasan Yoga na kasar Indiya, ya kuma gwada wasannin gargajiya na kasar Sin da ya koya kamar wasan takobi da wasan Taiji da wasan kokawa. Wani dan kallo wanda ya yi kallon wasan da Chen Ailong ya yi ya ce,

"A ganina wasannin da Ailong ya yi sun burge mu kwarai da gaske dalili kuwa shi ne yana kaunar wasannin motsa jiki na gargajiya na kasar Sin kuma yana kaunar al'adun kasar Sin."

Gwada gwanintarsa kan fasahar kasar Sin ya kara kwarin gwiwar Ailong dake zama a ketare kwarai da gaske. A cikin shekaru biyu da suka shige, kafofin yada labarai na kasar Sin da dama sun gayyace shi da ya shiga shirye shiryensu. Bi da bi ya shiga wasanni iri iri na nishadi da na shagugulan dare da gidajen talabiji na gwamnatin tsakiya na kasar Sin da na birnin Beijing da lardin Shanxi da Hunan da birnin Shenzhen suka shirya, wannan dan kasar Indiya da ya iya wasan Gongfu na kasar Sin ya samu kauna da furanni da kuma tafi daga 'yan kallo na kasar Sin. Duk da haka Ailong bai dakatar da kokarinsa na cika burinsa. A halin yanzu jadawalinsa na cike da ayyuka a ko wace rana. Bayan da ya kammala ayyukansa na samar da ilimi a makaranta, ya kuma gwada sabuwar gwanintar da ya koya. A matayinsa na mutum wanda ya yi shahara, ya shiga shirye shirye na gidajen talabiji na wurare dabam daban na kasar Sin. Da ya ke ya gaji kadan, yana jin dadin zaman hakan. Ya ce,

"Ina morewa zaman rayuwata a halin yanzu, da ya ke na sha aiki, zamana ya cike da karfin gwiwa da dadi da kuma sha'awa. Dalili kuwa shi ne yayin da ka kammala wani aiki sai ka jira mene ne wani aiki dabam mai zuwa, kana jin ma'anar zama. Wani sa'I ka gaji, amma wannan ya shaida maka cewa ka samu nasara, ka inganta kanka, abun da kake ji a wannan rana ya kuma shaida cewa burinka ya cika."

Mr Chen Ailong ya ce kasar Sin da Indiya kasashe ne makwabtan da juna, duwatsu da koguna sun hada su, haka kuma kasashe ne mafi kasaita daga cikin kasashe matasa a duniya. Sama da shekaru sittin da suka gabatar, likitan fida na Indiya Shantaram ya zo kasar Sin tare da kungiyarsa ta jinya mai ba da taimako ga kasar Sin, ya warkar da mutanen Sin da ke fama da cututtuka ko da wadanda suka ji rauni, ya ba da taimakonsa ga kasar Sin yayin da take yakar mahara japanawa. Har wa yau dai Mr Shantaram ya kasance jarumi ne a mutanen Sin da na Indiya. Mr Chen Ailong ya ce zai yi iyakacin kokarinsa wajen daukaka zumuncin dake tsakanin mutanen Indiya da na kasar Sin kamar yadda Mr Shantaram ya yi.

"Ina so in bude wani kamfanin da ya yi mu'amala tsakanin Indiya da kasar Sin a fannonin al'adu da fasaha da kuma kimiyya a nan gaba, ina so in zama wata gada wadda ta hada Indiya da Sin, in yi wasu abubuwa domin kara dankon zumuncin da ke tsakanin kasashen nan biyu da kara fahimtar mutanen Indiya kan kasar Sin. Ina fatan karin daliban Indiya da su samu damar shigar kasar Sin domin yin koyi da kasar Sin da al'adun kasar Sin da kuma fasaharta. Daliban kasar Sin za su iya zuwa kasar Indiya domin koyon fasahohin yanar gizo ta internet da kuma ilimin kimiyya, ta haka kuwa za su iya taimakon juna ta hanyar mu'amala."

A cikin shekaru da dama da yake aiki a kasar Sin, Shen Ailong ya zagaya wurare da dama na kasar Sin, ya kuma sami aminai sinawa masu tarin yawa. Kwarewar da ya samu a kasar Sin ya kara haske sosai ga rayuwarsa, yana jin zamansa a kasar Sin kamar ya yi zama a mahaifiyarsa. Ya ce,

"Yanzu ina jin kasar Sin kasata ce ta haihuwa, kuma ina jin tamkar a gidana. A nan ina da aminai da yawa, kuma ina da dalibai makaunata masu yawa, ina jin dadin zaman nan a kasar Sin."

A nan muna fatan daukacin bakin dake aiki da zama a kasar Sin suna jin dadin zamansu a kasar Sin kamar yadda Mr Chen Ailong wanda ya zo daga kasar Indiya ya yi.

Jama'a masu sauraro,wannan ya kawo karshen shirinmu na zaman rayuwar sinawa. Sai wannan lokaci na mako mai zuwa.(Ali)