Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-28 14:26:01    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin (14B)

cri

Kwaskwarima ta kawo mata matsala.Wata yarinya ta yi da na-sani a filin jirgin sama sabo da ta samu matsala wajen harkokin shige da fici.Wannan yarinya ta zo ne daga birnin Qingdao na lardin Shandong.ta yi karatu a kasar Faransa.Da ta dawo gida sai ta nemi a yi mata kwaskwarima,wato a gyara mata hanci.girar idanu da haba.Da ta gama ta dawo lafiya sai kuma tana so ta koma kasar Faransa ta ci gaba karatunta a can.Da ta je filin jirgin sama ta sami matsala,saboda hotonta a passport ya sha bamban da siffarta,shi ya sa ma'aikatan kwastam ba su yarda ta shiga cikin jirgin sama ba.sai ta koma gida ta samu dukkan takardun da suka shaida cewa abin da ta yi daga hukumomin da abin ya shafa suka bayar. Daga baya an tabbatar da matsayinta an ba ta iznin sake fita waje ta jirgin sama.

Kada ka ranta wa wani kudi. An sami wani mutum da ya ranta wa wani abokinsa kudi amma kuma yanzu yana so a taimake shi a mayar masa da kudinsa. Wannan mutumin ya zo ne daga birnin Qingdao na lardin Shandong na kasar Sin,sunan iyalinsa Zhao,ya ranta wa wani abokinsa kudin Sin RMB yuan dubu casa'in,kusan dukkan kudin da ya ajiye a cikin banki kafin shekaru goma da suka gabata.amma a yanzu abokinsa ya ki ya mayar da kudinsa ya ce jarinsa ya karye.Daga baya ya gabatar da abokinsa a gaban kotu,kotun ta yanke hukuncin ya mayar masa da kudinsa.Daga nan abokinsa ya bace.Da ganin haka,wannan mutum ya ba da sanarwar cewa duk mutumin da ya taimake shi aka mayar da kudinsa ,to zai ba shi lada da ya cancanci aikin da ya yi.

Kida ya warkar da maras lafiya. Kida ya komar da hankalin maras lafiya da ya ji rauni a cikin hadarin mota a birnin Shaoxing na lardin Zhejiang na kasa Sin.Sunan mutumin Li kuma ya samu mummunan rauni ne a cikin hadarin mota a watan Augusta daga nan ya kwanta a kan gado ba ci ba sha,amma yana raye.Da aka kai shi asibitin,likita ya binciki lafiyarsa ta injin duba kwakwalwa.Da aka buga masa kidan. Sai likitan ya gano wani abu ya motsa a kwakwalwarsa. Daga nan ana yi ta buga kida ga mutumin kuma, bayan watanni ya warke har yana iya magana da yawo da kansa.

An kama iyaye saboda suka tsare diyarsu. "yan sanda sun kama iyayen wata budurwa saboda sun kulle ta.Budurwar nan tana da shekaru sha takwas da haihuwa kuma ta shiga soyayya da wani.Iyayen ba su yarda ba sai suka daure budurwar a jikin gado suka rufe kofa.Wannan al'amari ya faru ne a birnin Zhengzhou na lardin Henan na kasar Sin. Da aka kulle ta,budurwar ta buga waya zuwa ga abokanta da 'yan sanda,Daga nan 'yan sanda suka zo wurin suka same ta a kulle.suka kubutar da ita daga gidan, suka kuma tafi da iyayen gidan wakafi.

---Wani saurayi ya ci tara sabo da ya shiga wata liyafa ba tare da izni ba.Kwanakin baya wani saurayi a birnin Baoding na lardin Hebei sabo da ya shiga wata liyafa da aka shirya domin bikin aure.Yayin da sabbin ma'aurata biyu suka daga kwaf suna masa godiya kan shiga liyafar sun ga alamun shan banban daga wannan mutum,sun shiga shakku da kirawo 'yan sanda.Da 'yan sanda suka yi masa tambaya,ya amsa laifinsa da cewa sau da yawa ya shiga burtun baki sa'an nan ya halarci liyafar da aka shirya domin bukukuwan aure.

---rigar barawo ta jawo hankalin masu gadi.An tsare wani mutum a gidan 'yan sanda sabo da ya yanke wayoyin da tsawonsu ya wuce mita dari hudu a wani wurin gina babban gini na birnin Shijiazhuang na lardin Hebei.Yayin da mutminnan ya fita daga kofa masu gadi sun ga mutumin nan ya sa babbar riga fiye da kima,suna tsammani watakila akwai wani abu a ciki.sai sun bukace shi da ya tube babbar riga.Da ya tube,ashe wayoyi ne na nannade a jikinsa.nauyinsu ya kai kilo ashirin,sai a tsare shi.

---An yanke hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan wakafi kan wani mutum da ya sayar da tabar jabu.An yanke hukuncin dauri na shekaru bakwai a gidan wakafi kan wani mutum a yankin Chaoyang na birnin Beijing sabo da ya tanadi tabar jabun da darajarsu ta kai kudin Sin miliyan 7.3 a gidansa.Sunan mutumin shi ne Shi Bi.A farkon wannan shekara,'yan sanda suka kama shi sabo da ya tuki wata motar dake dauke da taba.Daga baya an gano duk taban dake cikin motar na jabu ne.'Yan sanda sun kai samame a gidansa inda suka gano taban jabu masu yawan gaske.(Ali)