Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta zartas da shirin ba da jagoranci ga aikin farfado da gine-gine da suka rushe a bala'In dusar kankara da ruwan sama mai sanyi.
A ran 27 ga wata, cibiyar ba da umurni kan sha'anin kwal, da wutar lantarki, da man fetur, da sufuri, da kuma aikin ba da agaji da yaki da bala'I na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta gabatar da cewa, a cikin shirin an ce, ya kamata a farfado da manyan ayyuka na musamman tun da wuri, da kuma tabbatar da gine-gine na tsarin wutar lantarki da na zirga-zirga da na sadarwa da na zaman rayuwa suna aiki cikin daidaici.
A tsakiyar watan Janairu, an yi bala'in dusar kankara da ruwan sama a wuraren kudancin kasar Sin, wannan ya kawo illa mai tsanani ga aikin zirga-zirga, da aikin samar da makamashi, da zaman rayuwar jama'a da dai sauransu. (Zubairu)
|