Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-27 17:45:52    
Gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ba ta da hulda da harkokin siyasa

cri
A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, a bayyane ne wasu mutanen kasashen yammacin duniya sun saba da ruhun Olympics, wato ba a iya kulla hulda a tsakanin wasannin motsa jiki da harkokin siyasa ba, suna kulla hulda a tsakanin wasannin motsa jiki na Olympics da harkokin siyasa, har ma sun ce wai za su ki halartar gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing. Sabo da haka, a ran 24 ga wata, lokacin da shugaba Kipchoge Keino na kwamitin wasannin motsa jiki ta Olympics na kasar Kenya, kuma mamban kwamitiin wasannin motsa jiki na Olympics na kasa da kasa yake ganawa da wakilinmu da ke kasar Kenya, ya ce, gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ba ta da hulda da harkokin siyasa. Mr. Keino ya ce, "Ko shakka babu, kowane mutum, wato wani mamba ne na zaman al'umma da wata kasa bai gudu daga samu tasirin harkokin siyasa ba. Lokacin da muke horar da 'yan wasannin motsa jiki, bai kamata a sanya harkokin siyasa ko kadan a cikin zaman rayuwarsu ba. Ya kamata 'yan siyasa ne kawai za su daidaita harkokin siyasa. Abun da ya kamata 'yan wasan motsa jiki su mai da hankulansu a kai shi ne halartar gasar wasannin motsa jiki. Idan an kulla hulda a tsakanin wasannin motsa jiki da harkokin siyasa, za a saba da ruhun Olympics, kuma za a lalata wasannin motsa jiki na Olympics."

Game da huldar da ke tsakanin wasannin motsa jiki da harkokin siyasa, a fili ne an tsai da kuduri a cikin babi na 51 na "Babbar Dokar Olympics", cewar 'yan wasannin motsa jiki ba su iya furofganda bayanan siyasa da addinai da kabilu a wuraren gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ba. Amma yayin da aka soma kidaya rabin shekara da wani abu da suka rage da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing, wasu mutanen kasashen yammacin duniya sun dauki matakan karya Babbar Dokar Olympics da ruhun Olympics. Sun yi amfani da batun Darfur na kasar Sudan sun yi sharhi na rashin sanin ya kamata kan gwamnatin kasar Sin, har ma sun ce, wai za su ki halartar gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing. Amma yawancin nagartattun mutane masu aikin wasannin motsa jiki da 'yan siyasa na kasa da kasa sun yi suka kan irin wannan matakin da aka dauka da kakkausar harshe. Mr. Jacques Rogge, shugaban kwamitin wasannin motsa jiki na Olympics na kasa da kasa ya bayyana cewa, za a yanke hukunci kan wadanda za su ki halartar gasar wasannin motsa ta Olympics ta Beijing. Wani mutum daya kadai ya ki halartar gasar, ba zai lalata ingancin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ba. Mr. Rogge ya kuma cike da imani cewa, tabbas ne za a samu nasarar shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing. Shugaba George W. Bush na kasar Amurka ya kuma bayyana cewa, zai halarci gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing bisa shirin da ya tsara, kuma ba zai yi amfani da wannan gasar Olympics domin tattaunawa kan batun siyasa ba.

Tarihin gasannin wasannin motsa jiki na Olympics ya yi wa mutane gargadin cewa, za a samu hadari sosai idan an ki halartar gasar Olympics, wato za a kawo illa ga 'yan wasannin motsa jiki da gasar Olympics. Mr. Keino, wani tsohon magujin gudun dogon zango na kasar Kenya ya ce, "Mai yiyuwa ne ka tuna da gasar Olympics da aka shirya a birnin Moscow a shekarar 1980. Domin gwamnatin kasar Britaniya ta ki halartar wannan gasar. Sakamakon haka, dukkan 'yan wasannin motsa jiki na Britaniya ba su iya halartar wannan gasa ba. Amma dukkansu ba su mai da hankalunsu kan harkokin siyasa ba, sai gasar. Sun yi amfani da shekaru 4 domin share fagen wannan gasar. Bayan da ka yi amfani da kudade da yawa da lokatu da yawa wajen share fage, amma, kafin a kaddamar da wannan gasa, an gaya maka cewa, ba ka iya halartar wannan gasa, to, mene ne ganinka game da wannan ? An riga an sha wahala sosai domin sanya harkokin siyasa a cikin gasar Olympics."

A matsayin mamban kwamitin Olympics na kasa da kasa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, Mr. Keino ya zo kasar Sin har sau 3 a kowace shekara. Game da cigaban da birnin Beijing ya samu wajen shirya gasar, Mr. Keino ya ce,"Ina tsammani birnin Beijing yana shirya gasar bisa shirin da aka tsara kamar yadda ya kamata. Yanzu an riga an yi kusan kammala ayyukan gina dukkan filaye da dakunan wasannin motsa jiki da ake bukata, kuma ana gwajinsu kamar yadda ya kamata."

Daga karshe dai, Mr. Keino ya kirayi dukkan 'yan wasannin motsa jiki da wadanda suke aikin wasannin motsa jiki na kasa da kasa da su hada kan junansu, kuma su halarci gasar wasannin motsa jiki na Olympics ta Beijing. Sabo da haka, gasar Olympics za ta iya zama wani wurin da ake takara cikin adalci.