Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-27 15:30:12    
Hukumomin Beijing sun soma yin gyaran fuska ga wuraren tarihi domin masu ziyara a lokacin wasannin Olympics

cri

BEIJING. Beijing na shirin kashe kudin Sin Yuan miliyan 120 wato kimanin dalamiliyan 16 domin yin kwaskwarima ga wuraren tarihi na birnin ta yadda masu yawon shakatawa lokacin wasannin Olympics za su ga yadda wiyraren suke a zahiri .

Wuraren da za a musu kwaskwariman sun hada da haikalin Confucius, da kwalejin sarakuna da haikalin kakanin kakanin sarakuna da sauran wassu wuraren tarihi 28. Kamar yadda mataimakin darektan sashen kula da kayayyakin tarihi na birnin ya fadi.

Za a rubuta sunayen wuraren tarihi cikin harsunan Sinanci da turanci a muhimman wurare 300 da ke karkashin birnin kafin lokacin wasannin Olympics.

Haka kuma birnin ya buga takardu da taswirorin wuraren yawon shakatawa miliyan 6 cikin sinanci da turanci, ana kuma sa ran cxewar za a rarraba su a filayen jiragen sama da kauyen yanwasan da kuma hotel hotel da dakunan cin abinci a lokacin wasan.

Haka kuma gyaran fuskar ya hada da Siheyuan , wani tsohon matsugunin mutanen Beijing. Wadannan tsoffin wurare sun jawo hankulan masu yawon shakatawa a yan shekarunnan.(ilelah)