A ran 26 ga wata da dare agogon wurin, bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi masa, shugaban kasar Nijeriyar Umaru Musa 'yar Adua ya tashi zuwa kasar Sin don kai ziyarar aiki ta yini hudu.
Wannan shi ne karo na farko da Malam Umaru Musa 'yar adua zai kawo wa kasar Sin ziyara, tun bayan watan Mayu na shekarar da ta gabata, lokacin da ya hau karagar mulkin kasar. Bisa labarin da muka samu, a lokacin da yake ziyarar aiki a kasar Sin, zai yi shawarwari mai zurfi tare da shugabannin kasar Sin, kuma zai yi mu'ammala da mutane masu fadi-a-ji a bangaren masana'antu na Sin.(Bako)
|