Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-26 15:12:33    
Ziyarar da shugaban Nijeriya zai kawo wa kasar Sin na da muhimmanci sosai wajen raya dangantaka a tsakaninsu

cri
Ran 26 ga wata, shugaba Umaru Musa Yar'Adua na kasar Nijeriya ya tashi daga Nijeriya domin kawo wa kasar Sin ziyarar aiki. Wannan ne karo na farko da shugaba Yar'Adua zai kawo wa kasar Sin ziyara bayan da ya zama shugaban Nijeriya a watan Mayu na shekarar bara. A kwanan baya, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Lagos wato Bello, Ayo Olukanni, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Nijeriya ya bayyana cewa, ziyarar da shugaba Yar'Adua zai kawo wa kasar Sin tana da muhimmanci sosai wajen raya dangantaka a tsakaninsu.

Wannan kakaki ya nuna cewa, shugaba Yar'Adua yana fatan ziyararsa za ta inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 a fannoni daban daban. Ya ce,'Bisa tushe, shugaban Nijeriya zai yi wannan ziyara ne domin neman zurfafa dangantaka a tsakanin kasarsa da kasar Sin a fannoni daban daban, a ciki har da hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da siyasa da kuma al'adu.'

Nijeriya na matsayin ta biyu a Afirka ga kasar Sin a harkokin fice. Yanzu kasashen 2 suna nan kuma za su aiwatar da wasu manyan shirye-shiryen yin hadin gwiwa a tsakaninsu ta fuskar tattalin arziki da ciniki. Dimbin masana'antun kasar Sin masu karfi suna fuskantar kyakkyawar mako?a a Nijeriya. Kasar Sin za ta kuma kafa cibiyar al'adu ta kasashen Sin da Nijeriya a birnin Abuja. A lokacin ziyarar da shugaba Yar'Adua zai yi a kasar Sin, bangarorin 2 za su kara yin tattaunawa kan wannan batu. Sa'an nan kuma, za su daddale wata muhimmiyar sanarwa kan yin mu'amalar al'adu. Olukanni ya ce,'Za mu daddale 'daftarin tsari na shekarar 2008 zuwa ta 2010 kan aiwatar da hadin gwiwa da mu'amala a harkokin al'adu da aikin ba da ilmi' a tsakanin Sin da Nijeriya. Wannan zai zama muhimmin batu da zai jawo hankali a cikin ziyarar shugaba Yar'Adua.'

Tun bayan da kasashen Sin da Nijeriya suka kulla dangantakar diplomasiyya a shekarar 1971 har zuwa yanzu, sun raya dangantakar hadin gwiwa da zumunci a tsakaninsu kamar yadda ya kamata. Olukanni ya nuna gamsuwa kan ci gaban da kasashen 2 suka samu a yanzu wajen raya dangantaka a tsakaninsu. Ya ce,'A ganina, kasashen 2 suna kiyaye kyakkyawar sahihhiyar dangantaka domin moriyar juna a tsakaninsu. Dangantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare ta daukaka yin hadin gwiwa a harkokin tattalin arziki da siyasa da al'adu. Dukan bangarorin 2 sun gamsu da ci gaban dangantakarsu a yanzu.'

Baya ga ba da tasiri kan harkokin Afirka, Nijeriya tana jagoranci harkokin siyasa da tattalin arziki da tsaron kai a yankin Yammacin Afirka. Sin da ita sun sami ra'ayi daya a harkokin kasa da kasa da yawa. Za su yi hadin gwiwa a fannoni da yawa a nan gaba. Olukanni yana ganin cewa, kasashen Sin da Nijeriya suna da babban boyayyen karfi wajen samun bunkasuwa a nan gaba. Ya ce,'Ina tsammani cewa, har kullum kasar Sin, kawa ce ga Nijeriya da dukan kasashen Afirka, wadda aka iya gaskatawa ta da kuma dogara da ita. Kowa ya sani cewa, kasar Sin tana nuna sahihiyar kulawa kan bunkasuwar tattalin arziki na Nijeriya da ta kasashen duniya. An sami sakamako mai kyau a gun taron dandalin tattaunawa kan yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. kasar Sin tana bai wa kasashen Afirka taimako ta fuskar tattalin arziki da fasaha. Muna fatan irin wannan kyakkyawan sakamako zai ci gaba da kasancewa. Ziyarar da shugaba Yar'Adua zai kawo wa kasar Sin za ta kara samar wa Sin da Nijeriya karfi wajen inganta dangantaka a tsakaninsu.'

Ban da wannan kuma, Olukanni ya yi hasashen cewa, muhimmiyar ziyarar da shugaba Yar'Adua zai kawo wa kasar Sin za ta bude wa kasashen Nijeriya da Sin sabon shafi wajen raya dangantaka a tsakaninsu.(Tasallah)