Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-26 10:35:37    
Kasar Sin za ta kara karfi wajen binciken ingancin abincin da za a samar a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics

cri

Tun daga ran 25 zuwa ran 27 ga wata, hukumar sa ido kan ingancin abinci da magunguna ta kasar Sin ta hada kan sauran hukumomin gwamnatin kasar da su tura kungiyoyi 6 zuwa biranen Beijing da Tianjin da Shanghai da Qingdao da Shengyang da Qinghuangdao, inda za a yi gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing domin yin binciken yadda za a tabbatar da ingancin abinci a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics.

Tun daga tsakiyar kwanaki 10 na watan Disamba na shekarar da ta gabata zuwa karshen watan Janairu na shekarar da muke ciki, hukumar sa ido kan ingancin magunguna da abinci ta kasar Sin ta riga ta yi bincike kan yadda biranen da za su yi gasar wasannin motsa jiki ta Olympics suke tabbatar da ingancin abinci iri iri. Bisa sakamakon da aka samu, galibin matakan tabbatar da samar da ingancin abinci a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da wadannan birane suke dauka suna da kyau. (Sanusi Chen)