Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-26 09:27:29    
Firaministan kasar Birtaniya zai halarci wasannin Olympic na Beijing

cri
Ran 25 ga wata, a gun taron manema labaru da aka yi a Hongkong, ministan harkokin waje na kasar Birtaniya David Miliband ya bayyana cewar, kasar Birtaniya za ta halarci gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing daga dukkan fannoni, haka kuma, zuwa wancan lokacin, firaministan kasar Birtaniya shi ma zai halarci wannan gagarumin biki.

Ran 24 ga wata, Mr. Miliband ya isa Hongkong, kuma zai fara ziyararsa a kasar Sin a hukunce. Kafin Mr Miliband ya tashi daga Birtaniya, ya bayyana a kan tashar internet tasa wato blog cewa, yana sa ran kaiwa kasar Sin ziyara, kuma yana adawa ga dukkan aikace-aikace na yi wa kasar Sin matsin lamba bisa ga gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing.

A gun taron manema labaru, Mr. Miliband ya bayyana cewa, ba ma kawai mutanen kasar Sin za su ci gajiya daga bunkasuwar Sin ba, har ma tattalin arziki na dukkan duniya zai sami babbar moriya. Ya kamata gamayyar kasa da kasa su kara fahimta kasar Sin, ga shi kuma yanzu, kalubalen da kasar Sin ke fuskanta, su ma, tarayyar kasashe masu arzikin masana'antu da tarayyar kasashe masu saurin bunkasuwa su ma suna fuskanta tare.

Dadin daddawa kuma, ya bayyana cewa, nasarorin da birnin Hongkong ta samu, bayan dawowarta kasar Sin shekaru 10 da suka gabata, yana ba da mamaki sosai, ga shi kuma ya soki dukkan hasashen da wasu mutane masu nuna shakku a kan makomar Hongkong suka yi mata.(Bako)