Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-25 20:59:11    
Wasu labarai na kananan kabilun kasar Sin

cri

Jama'a masu sauraro, muna muku marahabin da sauraran shirinmu na "Kananan kabilun kasar Sin." Yanzu kuma za mu kawo muku wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin.

---- Domin tunawa da "wurin da aka fara wasan skiing na 'yan adam", kwanan baya an shirya gasar skiing a kan dusar kankara a yankin Aletai na jihar Xinjiang da ke kuryar arewa ta kasar Sin.

A gun gasar da aka yi, 'yan wasan da suka zo daga kananan kabilu daban-daban na wannan wuri sun yi amfani da kayan wasan gargajiya da suka kera da kansu, suna yin gasa kan dusar kankara wanda zurfinsa ya wuce centimita 10. Ban da wannan kuma an bude lambun yin sassakar kankara ko dusar kankara, da yin wasannin motsa jiki masu ban sha'awa cikin gandun daji, dukkan wadannan wasanni sun jawo hankulan masu yawon shakatawa da yawa.

An ce, takardar sunayen Guinness ta birnin Shanghai na kasar Sin ta tabbatar da cewa, yankin Aletai na jihar Xinjiang ta kasar shi ne ya fi dadewa wajen yin wasan skiing a kan dusar kankara na 'yan adam.

---- Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin ta yi kokarin bunkasa makamashin halittu, kuma ta mai da muhimmanci wajen raya makamashin bola jari wato makamashin da ake iya samu kullum a kauyuka ciki har da irin gas da aka samu daga bola, da makamashin da ake samu ta hanyar hasken rana da iska.

Bisa kididdigar da aka yi an ce, a halin yanzu yawan mutanen jihar Tibet da suke yin amfani da makamashin gas da aka samu daga bola ya kai dubu 125, kuma mutane fiye da miliyan 2.5 sun yi amfani da makamashin da ake samu ta hanyar hasken rana domin dafa abinci. Ban da wannan kuma, an samu babban ci gaba wajen ba da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da makamashin iska. Makamashin bola jari wato makamashin da ake iya samu kullum ba ma kawai ya kyautata muhallin halittu masu rai da ingancin zaman rayuwar manoma da makiyaya ba, kuma ya kara daidaita tsarin aikin noma da kiwon dabbobi, da kara samar da kudin shiga da yawa ga manoma da makiyaya.

---- Zuwa karshen shekarar da ta wuce, an kusan tabbatar da makasudin samun ilmi tilas na makarantu masu tsarin karatu na shekaru 9 da yaki da jahilci ga samari da manya a jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin

Wakilinmu ya samo wannan labari ne kwanan baya daga wajen gwamnatin jihar. An ce, cikin shekaru 5 da suka wuce, jihar Tibet ta kammala aikin ginawa da yin gyare-gyaren makarantun firamare na gundumomi da garuruwa wadanda yawansu ya wuce 400, da haka ne aka daidaita matsalar rashin dakunan koyarwa da na zaman yau da kullum na 'yan makaranta da yawansu ya kai kusan dubu 40. A sa'i daya kuma, jihar Tibet ta yi matukar kokari domin kyautata sharudan makarantu, zuwa karshen shekarar bara, kashi 90 bisa 100 na dukkan makarantun faramare na jihar sun yi aikin koyawa ta hanyar zamani.