Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-25 15:46:27    
Za a samun kyakkyawan yanayi a lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri

A kwanakin baya, bayan da hukumar kula da yanayin sararin samaniya ta birnin Beijing ta yi nazarin tarihin yanayin da ake ciki a watan Agusta na shekaru 30 da suka wuce a nan birnin Beijing, ta yi nuni da cewa, za a samun yawan zafi na digiri celsius 24.9 a kiyasce lokacin da ake yin gasar wasannin Olympic ta Beijing, wannan yana da kyau.

A kwanakin baya, akwai kafofin watsa labaru na kasashen waje da suka ce wai a ko wane watan Agusta, za a yi zafi da gumi sosai a birnin Beijing, wannan ba ya da kyau ga gasar.

Mr. Guo Wenli direkatan cibiyar yanayi ta hukumar kula da yanayin sararin samaniya ta birnin Beijing ya ce, mutane ba za su ji zafi da gumi sosai ba. Tun ran 7 ga watan Agusta, yawan zafi da yawan gumi za su ragu a birnin Beijing, za a shiga lokacin jin dadin yanayi, wato lokacin kaka sannu sannu. Bisa kididdigar da aka yi kan "yawan zafi", yawan zafi da za a yi a lokacin gasar wasannin Olympic na Beijing ta yi daidai kamar yanayin zafi da aka yi a lokacin gasar wasannin Olympic ta Barcelona, kuma ya fi kyau ga Atlantis da Athens.

Bayan da aka shiga lokacin kaka a nan kasar Sin, yanayi ya fi kyau. Saboda haka, za a samu yanayi mai kyau yayin da ake yi gasar wasannin Olympic na nakasassu.