Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-23 16:50:09    
Kasar Sin za ta yi amfani da dokoki wajen kare gasar wasannin motsa jiki ta Olympics

cri
A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasar Si ta tsara jerin dokoki da ka'idoji domin tabbatar da kare gasar wasannin motsa jiki ta Olympics a karo na 29 da za a yi a nan birnin Beijing a shekarar 2008.

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, birnin Beijing ya riga ya tsara kuma bayar da "dokar kare ikon mallakar ilmi na Olympics" da "ka'idojin tabbatar da kwanciyar hankali a gun bukukuwan jama'a masu girma" da dai makamatansu. Bugu da kari kuma, an riga an bayar da dokoki da ka'idojin da suke da nasaba da fannoni iri daban-daban, kamar su masu aikin sa kai da rediyo da kiwon lafiya da ingancin abinci, kuma an yi kwaskwarima kan ka'idar sa ido kan harkokin yawon shakatawa da tabbatar da ingancin muhalli.

Ban da birnin Beijing ya tsara, kuma ya bayar da wasu dokoki da ka'idoji, kasar Sin ma ta tasra, kuma ya bayar da wasu ka'doji da dokoki a matsayin kasa, kamar a shekarar 2002, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayar da "ka'idojin kare alamun Olympics". Sannan kuma, wasu hukumomin gwamnatin kasar Sin sun bayar da jerin ka'idoji bi da bi domin kare ikon mallakar ilmin Olympics. (Sanusi Chen)