A shekarar 2008, birnin Beijing zai kara kyautata tsarin samar da kwal da wautar lantarki da man gas da man fetur domin tabbatar da samar da isassun makamashi a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics.
A ran 22 ga ga wata, Mr. Zhang Gong, direktan kwamitin yin gyare-gyare da cigaban birnin Beijing ya bayyana cewa, za a sarrafa yawan makamashin da za a yi amfani da shi a nan birnin Beijng a shekarar 2008 da yawansu zai kai kamar kwal ton misalin miliyan 65. Yawan makamashin da za a yi amfani da shi domin samun kowane GDP kudin Renminbi yuan dubu 10 zai ragu da kashi 5 cikin kashi dari.
Bisa shirin tabbatar da samar da makamashi, yawan wutar lantarki da birnin Beijing zai tabbatar da samarwa a shekarar 2008 zai kai kilowatts miliyan 14.6, a waje daya kuma, za a yi kokarin tabbatar da samar da man gas da yawansa zai kai kubik mita miliyan 680 domin tabbatar da samar da tsabtaccen makamashi a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing. (Sanusi Chen)
|