Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-22 20:20:00    
China za ta bayar da tallafin aiki gona kai tsaye domin sake gina wuraren da suka sha fama da bala'i

cri

China tana turawa da biliyoyin Yuan a matsayin kudin tallafin aikin gona, tun gabanin faduwar damina, a wuraren da suka sha fama da bala'in dusar kankara, domin taimaka masu wajen yin huda, a matsayin wani bangare na sake gina wadannan wurare da bala'in dusar kankarar ya yiwa mummunar illa.

Ma'aikatar kula da harkokin kudi ta kasar Sin, ita ce ta sanar da hakan jiya Alhamis, inda ta kara da cewa a ranar Labara ne aka tura da adadin kudi na Yuan biliyan 63.3, wato dala biliyan 9.04, zuwa ga larduna da kuma yankuna masu cin gishin kansu, wadanda bala'in ya yiwa ta'adi, a matsayin kudin tallafi na aikin gona.

China dai ta sha alwashin gaggauta aikin sake farfado da harkokin aikin gona, a matsayin wani yunkuri na yin kyakyawan shiri na tunkarar aikin gona, da kuma tabbatar da samar da amfanin gona yadda ya kamata a wannan shekara.

A cewar ma'aikatar kudin ta China, gwamnati tana aiki tukuru, wajen bayar da fifiko ga manufofin aikin gona, cewa wadanda suka shuka hatsi da kuma bangaren masana'antu masu sayen kayan aikin noma, zasu samu tallafi kai tsaye kuma cikin lokaci. [Lawal]