Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-22 18:18:35    
Matsayin gwamnatin Sin kan batun Darfur

cri
Ran 21 ga wata, Liu Guijin, wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin mai kula da batun Darfur ya kira taron manema labaru a birnin London, hedkwatar kasar Birtaniya, inda ya yi karin bayani kan ci gaban batun Darfur, ya kuma bayyana matsayin gwamnatin Sin kan wannan batu, sa'an nan kuma, ya amsa tambayoyin da manema labaru na Sin da sauran kasashe suka yi masa.

Da farko Liu ya yi bayani kan kokarin da gwamnatin Sin take yi domin warware batun Darfur. Ya kuma yi nuni da cewa, a daidai sakamakon kokarin da kasar Sin da kasashen duniya suke yi, gwamnatin kasar Sudan ta amince da jibge hadaddun sojojin kiyaye zaman lafiya a Darfur, haka kuma, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da kuduri mai lamba 1769, ta haka an maido da batun warware matsalar Darfur a kan hanya kamar yadda ya kamata. Liu ya ce,'Batun Darfur na da sarkakkiya, ana bukatar bangarori a kalla 5 da su yi kokari tare domin warware batun. Da farko shi ne gwamnatin Sudan, na biyu shi ne dakarun da ba sa ga maciji da gwamnatin. Ina fatan za su komo kan teburin shawarwari cikin sauri, saboda ba za a sa aya ga tarzoma a wurin da kyautata tsaron lafiya da kuma jibge hadaddun sojojin kiyaye zaman lafiya yadda ya kamata ba, in ayyukan siyasa ba su cimma tudun dafawa ba, kuma gwamnatin da dakarun da ba sa ga maciji da gwamnatin ba su sami ra'ayi daya ba. Na uku shi ne kasashen duniya. Ya zuwa yanzu ana fuskantar matsalolin fasaha wajen jibge hadaddun sojojin kiyaye zaman lafiya. Na hudu shi ne kasashen da suke kasancewa a yankin iri daya da Sudan da kuma wadanda ke makwabtaka da Sudan. Na biyar shi ne kungiyar tarayyar Afirka wato AU da Majalisar Dinkin Duniya. Ya kamata su yi amfani da tsarin yin shawarwari a tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar AU da Sudan domin gaggauta ayyukan da warware wasu matsaloli na rashin fahimtar juna da matsalolin fasaha.'

Game da babbar akida da gwamnatin Sin ke bi wajen daidaita batun Darfur, wannan jami'in Sin ya ce,'Babbar akida da gwamnatin Sin ke bi ita ce girmamawa mulkin kan Sudan da cikakken yankin Sudan. Ita kuma babbar akida ce da ya kamata a bi wajen warware batun Darfur da batun Sudan da hargitsin yankuna da abin ya shafa. Ina farin ciki saboda kasashen Amurka da Birtaniya da kungiyar tarayyar Turai da sauran kasashe da yawa sun amince da wannan akida. Ga misali, a lokacin da kasar Sin take shugabancin kwamitin sulhu, an zartas da kuduri mai lamba 1769 a ran 31 ga watan Yuli na shekarar bara. Amma a wani bangare daban, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan ganin gwamnatin Sudan za ta amince da kudurin. In babu goyon baya daga gwamnatin Sudan, to, ba a iya gudanar da kudurin ba. A sakamakon warware batun Darfur, kasar Sin za ta nuna ra'ayi mai yakini, za ta kuma kara daukar nauyin da ake danka mata da kara taka rawarta a kan warware rikici a tsakanin kasashe masu tasowa, wanda ya yi kama da batun Darfur. Kazalika kuma, gwamnatin Sin ta gano cewa, baya ga warware batun cikin himma, dole ne a yi la'akari da kulawar da bangarori daban daban suke nunawa. In ba haka ba, ba za a iya warware wannan batu ba.'

Liu ya ci gaba da cewa, shugabannin kasashen yammacin duniya ba su zargi kasar Sin bisa batun Darfur ba a gun ganawa a tsakaninsu da shugabannin kasar Sin, ko kuma a cikin sanarwoyin da suka bayar a hukunce. Amma duk da haka, sun gabatar da shawarwari masu kyau ga kasar Sin.

Dangane da yunkurin kaucewa gasar wasannin Olympic ta Beijing bisa batun Darfur, Liu ya bayyana cewa,'Kullum na kan ce, Darfur ba na kasar Sin ba ne, haka kuma, batun Darfur ba ruwan kasar Sin ba. Shi ya sa hada da wadannan batutuwa 2 a wuri daya ba shi da kan gado ko kadan. Ban da wannan kuma, yanzu wasu adalan mutane na kasashen duniya sun lura da lamarin. In kasashen duniya suka karfafa gwiwa a shirya gasar wasannin Olympic ta hanyar siyasa, to, a cikin dogon lokaci za a kawo hadari. Ga misali, London za ta shirya gasar wasannin Olympic a shekarar 2012. In a lokacin can, wasu sun gabatar da wasu abubuwa ba ruwan da gasar wasannin Olympic, tabbas ne London za ta shiga halin kaka-ni-ka-yi.'(Tasallah)