Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-22 15:45:20    
Labari mai ban sha'awa a game da gasar wasannin Olympics ta farko a zamanin yanzu

cri

Aminai 'yan Afrika, a makon jiya dai, mun rigaya mun dan gutsura muku wani bayani kan gasar wasannin Olympics ta farko a zamanin yanzu da aka gudanar a kasar Girka. Yau dai, za mu ci gaba da hira kan wannan gasa. Ko da yake an gudanar da gasar wasannin Olympics ta farko ta zamanin yanzu, amma tasirin da ta yi, kalilan ne.

A shirinmu na makon jiya dai, mun taba gaya muku cewa, zakaran farko a tarihin wasannin Olympics na zamanin yanzu shi ne dan wasa mai suna James Connolly daga kasar Amurka, wanda ya zo na daya a gun gasar tsallen nesa na yin dira 3 da tsawon mita 13 da digo 71. Amma abun bakin ciki shi ne Jami'ar da yake yin karatu a can ta kore shi daga Jami'ar yayin da yake koma wa kasa tare da lambar zinariya ta wasannin Olympics domin kuwa shi Connolly wanda ya kasance wani dalibi na aji na biyu na Jami'ar din a wancan lokaci bai samu izinin zuwan kasar Girka don shiga gasa ba. Wannan dai ya shaida cewa, ya zuwa karshen karni na 19, mutane masu tarin yawa ba su gane gasar wasannin Olympics ba tukuna. Tuni a lokacin da ake kiran gasar wasannin Olympics ta farko ta zamanin yanzu, gwamnatin kasar Girka ta bada goron gayyata ga kasashe daban-daban ciki har da kasar Sin. Amma yawancinsu ciki har da kasar Sin ba su tura kungiyoyinsu don halartar gasanni ba bisa dalilin rashin fahimtar gasar wasannin Olympics ko kuma sauran wasu musababbi. Kasar Italiya wato makwabtaciyar kasar Girka ta aika da dan wasa daya tilo.

Yanzu, mun san cewa, an shirya manyan ayyukan wasanni iri 9 da kuma kananan ayyukan wasanni iri 43 a gun gasar wasannin Olympics ta farko a wancan zamani, wadanda suka hada da wasan guje-guje da tsalle-tsalle, da wasan sukuwar keken hawa, da wasan ninkaya, da wasan lankwashe jiki wato Gymnestics, da wasan kokawa irin na gargajiyar Roma, da wasan kwallon tennis, da wasan takobi, da wasan daga nauyin karafa da kuma wasan harba kibiya. Amma, wani bayanin da abun ya shafa na tarihi da aka bayar a zahiri na yin nuni da cewa, da ma kwamitin shirya wasannin Olympics na wancan gami ya shirya gasar wasan tseren kwale-kwale. Amma ya soke shirin a karshe bisa dalilan cewa yanayi ba kyau a wancan lokaci ko ma ba wanda ya yi rajistan shiga gasar. An gudanar da gasar wasannin Olympics ta farko ne a ranar 6 ga watan Afrilu na shekarar 1896 wato daidai lokacin bude wannan gasa.

Abin da muke so mu gaya muku, shi ne an kaddamar da gasar tsallen gora a gun wasan guje-guje da tsalle-tsalle na gasar wasannin Olympics ta farko da aka gudanar tun wancan lokaci, inda 'yan wasa na kasar Amurke ne kawai suka tafi sun bar sauran 'yan wasa daga kasashe daban-daban na duniya baya.(Sani Wang)