Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-21 16:56:25    
Kusoshi fiye da 100 daga kasashe 80 ko fiye na duniya za su halarci bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri
Ran 21 ga wata, a gun taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, Liu Jianchao, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu shugabannin kasashe da shugabannin gwamnatocin kasashe da mambobin masarauta fiye da 100 da suka fito daga kasashe sama da 80 a duk duniya sun bayyana fatansu na halartar bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing a shekarar 2008 da muke ciki. Kasar Sin tana maraba da su da hannu biyu biyu.

An labarta cewa, shugaba George Walker Bush na kasar Amurka da shugaba Nicolas Sarkozy na kasar Faransa da sauran kusoshin kasa da kasa sun bayyana cewa, za su halarci bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing.(Tasallah)