Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-21 15:00:33    
Ana farfado da `hanyar cinikin siliki`

cri

Yau da shekaru fiye da dubu biyu da suka shige,wata hanya mai yin cinikin siliki ta kara cudayar kayayyaki da al`adu dake tsakanin kasashen yamma da kasashen gabas,ita ma ta kawo wadatuwa ga shiyyar Asiya da Turai wadda ke da nisa daga teku.Yau ma,ana so a sake farfado da wannan hanyar yin cinikin siliki,ta yadda za a kafa wata hanyar sufuri ta zamani tsakanin Asiya da Turai,kasashen dake bakin wannan hanya suna yin maraba kuma suna goyon bayan wannan aiki kwarai da gaske.

A gun babban taro na 3 na hanyar cinikin siliki ta duniya da aka kira a birnin Xi`an na lardin Shaanxi na kasar Sin,wato birni mafarin tsohuwar hanyar yin cinikin siliki,wakilai da suka zo daga kasashen dake bakin hanyar cinikin siliki da kungiyoyin duniya sun tattauna kan mafarkinsu na farfado da hanyar cinikin siliki,gaba daya suna ganin cewa,wajibi ne a gina wannan hanyar sufuri ta zamani saboda ko shakka babu wannan hanya za ta kara ingiza bunkasuwa da wadatuwa a nahiyar Asiya da Turai.

Tsohuwar hanyar yin cinikin siliki ta fara ne daga kasar Sin,ta hada nahiyar Asiya da nahiyar Turai,tsawonta ya kai fiye da kilomita dubu bakwai,cudanyar dake tsakanin Asiya da Turai ta ba da babban amfani ga bunkasuwar tattalin arziki da al`adu da zamantakewar al`umma ta kasar Sin da kasashen dake tsakiyar Asiya da kasashen Turai.Saboda dalilin tarihi,wannan hanya ta taba daina aiki.

Yanzu,bisa bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin,hanyar cinikin siliki ta sake fara aiki,amma,a zamanin da,mutane sun yi amfani da doki da rakumi domin yin jigilar kayayyaki wato siliki da sauransu,yau dai,dole ne hanyar nan ta biya bukatun sufuri na zamani,amma akwai wuya a halin yanzu,musamman ma daga kasar Turkey zuwa kasar Iran da kasar Turkmenistan da kasar Uzbekistan da kasar Kazakhstan da kasar Kyrghyz har zuwa kasar Sin.

A karkashin irin wannan hali,kafin shekaru bakwai da suka shige,kawancen hanyar jirgin kasa na duniya ya ba da shawara cewa,kamata ya yi a farfado da `hanyar cinikin siliki`.Sabuwar hanyar cinikin siliki ta fi tsohuwar hanyar cinikin siliki tsawo kuma ta fi ta fadi.Wato gabashin mafarinta shi ne birnin Lianyungang na lardin Shandong na kasar Sin,wuri mai nisa a yammacinta shi ne birnin Rotterdam na kasar Holand,wato ta hada kasar Sin da sauran kasashe da shiyoyi fiye da arba`in na tsakiyar Asiya da Turai,nisanta ya kai fiye da kilomita dubu goma,saboda haka an mayar da ita a matsayin babbar hanyar tattalin arziki mafi tsawo a duniya wadda ke da boyayyen karfin bunkasuwa mafi girma.

Da zarar an gabatar da wannan shawara game da farfadowar hanyar cinikin siliki,sai ta sami goyon baya daga wajen kasashe da kungiyoyin duniya da yawa dake bakin hanyar.A gun babban taro na 3 na hanyar cinikin siliki na duniya,ministocin sufuri da suka zo daga kasashe 12 sun yi bayani kan muhimmiyar ma`ana ta `hanyar cinikin siliki` ga bunkasuwar tattalin arzikin kasashensu da harsuna dabam daban.

Kasar Sin da kasashen Turai su ma za su kafa sabuwar kasuwa,kuma za su yi amfani da albarkatai masu arziki na shiyyar dake tsakiyar Asiya.Wannan yana da muhimmiyar ma`ana ga bunkasuwar yammancin kasar Sin.Ko shakka babu sabuwar hanyar cinikin siliki za ta zama kadarkon cudanya dake tsakanin nahiyar Asiya da Turai.