Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-21 14:52:22    
Masar ta yi kokarin zama jigon tattalin arzikin Afrika

cri

Asalam alaikum jama'a masu sauraro, barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa da ku a wannan shiri namu na Afrika a yau. A cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wani bayani a kan cewa Masar ta yi kokarin zama jigon tattalin arziki na Afrika.

Ga bakin da ke zama a kasar Masar a kullum,abin da ya fi daukar hankulansu shi ne ci gaban tattalin arzikin kasar Masar. A cikin shekaru uku da 'yan kai da wakilin jaridar « people's daily » ta kasar Sin ke aiki a birnin Alkahira, farashin musayar kudi tsakanin dalar Amurka da kudin Pound na Masar ya kasance daya da shida da digo uku (1 :6.3), a halin yanzu ya kai daya da biyar da digo biyar (1 :5.5), darajar kudin Masar ta kara karfi a shekarun baya, masana na Masar sun yi hasashe cewa kudin Pound na Masar zai ci gaba da kara daraja.

Darajar kudin pound ta kasar masar ta shaida juyi da bunkasuwa da aka samu na tattalin arzikin kasar Masar, sun kuma kara karfin kwarin gwiwar mutanenta kan makomarsu.

Aran 9 ga watan Satumba na shekara ta 2007, yayin da firayim minista Nazif na kasar Masar ya gana da baki daga kasar Italiya, ya ce tare da ci gaba da kokarinta na yin kwaskwarima, Masar ta hada kanta da sauran kasashen duniya wajen tattalin arziki, za ta shiga sahun gaba na kasashe masu cigaban masana'antu a duniya a shekara ta 2020 za ta zama jigon tattalin arziki a nahiyar Afrika.

Shugaban kasar Masar Mubarak ya yi jawabi haka firayim ministan kasa Nazif ya yi jawabi a majalisar dokoki a karshen shekarar bara da farkon wannan shekara, dukkansu sun bayyana niyya da imani na kasar Masar a sabuwar shekara na dosawa gaba bisa manufar da aka tsara, ta kuma dauki matakan da ya wajaba. Su ci gaba da yin gyare gyare a fannin tattalin arziki da rubanya kokarinsu na bunkasa tattalin arziki a fagagge daban daban, da inganta yanayin zuba jari da habaka hanyoyin da saukaka hanyoyin da ake bi wajen shiga da jarin waje,su kokarta wajen bunkasa masana'antu, da dora muhimmanci kan aikin gona, da kara bunkasa ayyukan makamashi da kudade da al'adu da tarbiyya da yawon shakatawa da kuma muhalli, A sa'i daya kuma ta rika samar da sabbin guraban aiki da rage yawan marasa aikin yi.

A cikin shirinta na raya kasa na shekaru biyar biyar watau daga shekara ta 2007 zuwa shekara ta 2012, Masar ta tsara karin tattalin arzikin kasa da kashi 8 bisa dari a kowace shekara,a sa'i daya kuma za ta tabbatar da karin tattalin arziki da ninki daya a cikin shekaru biyar masu zuwa,wato daga kudin Pound na Masar biliyan dari bakwai a shirin kudi na shekara ta tsakanin 2006 da 2007 zuwa kudin pound na Masar biliyan 1350 na shirin kudi na shekara ta tsakanin 2011 da 2012. A sa'i daya kuma kasar Masar za ta yi shirin kara zuba jari na kudin Pound biliyan 1200 da samar da guraban aiki dubu dari takwas da ragen yawan marasa aikin yi daga kashi 9 bisa dari zuwa kashi biyar bisa dari.

Daukacin tattalin arziki na Masar a shirin kudi na shekara ta 2006/2007 ya samu ci gaba yadda ya kamata, jimlar kudin kayayyakin da ake samarwa a gida watau GDP ya kai dalar Amurka biliyan 111. Karo na farko ne a cikin shekaru sama da talatin da suka gabata karin tattalin arzikin kasa ya wuce kashi bakwai bisa dari watau ya kai kashi 7 da digo biyu bisa dari, kwatankwancin kudi na GDP na kowane mutum ya kai dalar Amurka dubu daya da dari biyar da sha takwas,watau ya karu da kashi 5 da digo takwas bisa dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara. A sa'i daya Masar ta kasance kasar da ta fi jawo jarin waje a nahiyar Afrika. Shekara ta 2008,shekara ce mai muhimmanci ga kasar Masar, ta yaya ta sanya tattalin arzikinta na ci gaba da karuwa bisa matakin na shekara ta 2007,jarrabawa ce ga gwamnatin Masar. Alal misali kan yawon shakatawa wanda gwamnati ke mallaka kuma ginshikin tattalin arzikin kasa da wani mafarin kudin shiga, yawan masu yawon bude idanu a kasar Masar a shekarar bara ya kai miliyan 11,kudin da aka samu ya kai dalar Amurka sama da biliyan tara, yawan masu yawon shakatawa da kudin da aka samu a shekara bara sun kai matakin koli a tarihi. Gwamnatin Masar ta yi shirin jawo baki masu yawon shakatwa miliyan 25 har zuwa shekara ta 2020, ta yaya za ta ci gaba da kai sabon mataki da kuma cika burinta,babbar dawainiyya ce ga gwamnatin Masar. A halin yanzu ma'aikatun kula da harkokin yawon shakatawa na Masar suna nan suna nazarin sabbin dabarun samun yawan masu yawon bude idanu da tabbatar da su, ban da yawon shakatawa a wurare masu kyaun gani da na tarihi da harkokin al'adu da dabi'u, ta kuma gabatar da shirye-shiryen yawon shakatawa na kiwon lafiya da gina lafiyar jiki da kuma na hamada da ba a taba aiwatar da su a da ba duk domin jawo hankulan baki masu sha'awar yawon shakatawa.

A cikin rahotonsa bankin duniya ya mai da kasar a kan matsayin kasa da ta fi samun ci gaba wajen kawo sauyi a duniya a shekara ta 2007, tana kan matsayin kasa ta 26 daga cikin kasashe 178 na duniya, a bangaren gabas ta tsakiya tana bayan hadaddiyar daular Larabawa da Isra'ila kawai. A tsakiyar watan Disamba da ta shige yayin da shugaban bankin duniya ya yi rangadi a kasar Masar ya yi nuni da cewa Masar ta samu babban ci gaba wajen yi wa tattalin arzikinta kwaskwarima, ta isa abar koyi ga kasashe masu tasowa. Ana sa ran cewa a sabuwar shekara, tattalin arzikin Masar zai kara samun ci gaba, ta aza tushe mai kyau da ta zama damisar tattalin arzikin nahiyar Afrika tun tuni.

Jama'a masu sauraro,wannan dai ya kawo karshen shirinmu na Afrika a yau, mun gode muku sabo da kun saurarenmu.Malam Ali ya shirya wannan shirin, Malam Balarabe ya karanta. (Ali)