Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-21 13:14:15    
Wasu shugabannin kasashe sun ci gaba da nuna jejeto ga wuraren da ke fama da bala'in dusar kankara a kudancin kasar Sin

cri
Kwanakin nan, wasu shugabannin kasashen waje sun ci gaba da aiko da sakon nuna jejeto ga shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao da kuma shugaban zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin Mr.Wu Bangguo da Wen Jiabao firayim minista na majalisar gudanarwa na kasar Sin, inda suka nuna babban juyayi ga wuraren da ke fama da bala'in dusar kankara a kudancin kasar Sin.

Shugabannin da suka aiko da sakon, sun hada da shugaban kasar Cameroon Paul Biya da takwaransa na kasar Afrika ta tsakiya Bozize da na kasar Guinea-Bissau Vieira da na kasar Ghana Kufuor da na kasar Gabon Bongo da dai sauransu. Dukkansu sun yaba da matakan da kasar Sin ta dauka wajen yaki da bala'i da kuma taimaka wa mutane da abin ya shafa, da aikin sake gina wurare da bala'in ya shafa, kuma sun yi imani cewa, gwamnatin Sin da jama'arta suna da kwarewa wajen sake farfado da zaman rayuwar jama'a da kuma aikin kawo albarka tun da wuri.

Ran 20 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Liu Jianchao ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun yi godiya ga dukkan gwamnatocin kasashe daban daban da kuma jama'arsu da suka nuna kulawa da goyon baya ga yaki da bala'i da kuma taimaka wa mutanen da bala'in ya shafa a kasar Sin.(Bako)