Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-20 21:26:36    
Kasar Sin tana son daukaka ci gaban dangantaka a tsakaninta da Japan yadda ya kamata

cri
Ran 20 ga wata, a nan Beijing, Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin tana son gama kanta da kasar Japan domin yin kokari wajen daukaka ci gaban dangantaka a tsakanin kasashen 2 ba tare da tangarda ba.

A lokacin da yake ganawa da tawagar majalisar dattawa ta Japan mai halartar taro na karo na 2 a Beijing bisa tsarin yin mu'amala a tsakanin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da majalisar dattawa ta Japan a lokaci-lokaci, Wu Bangguo ya ce, shekarar bana muhimmiyar shekara ce a tarihin raya hulda a tsakanin Sin da Japan. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin zai kai wa Japan ziyarar aiki, wannan ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya kai wa Japan ziyara a cikin sabon karni. Shugaba Hu zai tsara kyakkyawan tsari tare da takwaransa na Japan kan raya hulda a tsakanin kasashen 2, wannan na da muhimmiyar ma'ana mai zurfi a fannin bunkasa hulda a tsakanin wadannan kasashe 2.

Bugu da kari kuma, wannan jami'in Sin yana fatan kasashen Sin da Japan za su ci gaba da yin amfani da wannan muhimmin tsarin yin mu'amala domin ba da kyakkyawar gudummowa wajen raya dangantakar aminci a tsakanin Sin da Japan yadda ya kamata ba tare da tangarda ba.

A nasa bangaren kuma, Oishi Masamitsu, shugaban tawagar majalisar dattawa ta Japan ya ce, majalisar dattawa ta Japan za ta ci gaba da yin kokari ba tare da kasala ba wajen kara fahimtar juna da aminci a tsakanin jama'ar Sin da Japan da kuma habada hadin gwiwa a fannin kiyaye muhalli da dai sauransu.(Tasallah)