Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-20 16:28:42    
An giggina filaye da dakunan gasar wasannin Olympics duk bisa babbar bukatar tsare-tsaren birnin Beijing

cri
Mataimakin daraktan kwamitin raya birnin Beijing Zhang Jiaming ya fadawa kafofin yada labarai na gida da na ketare jiya 19 ga wata cewar, an giggina filaye da dakunan gasar wasannin motsa jiki ta Olympics duk bisa babbar bukatar tsare-tsaren birnin Beijing daga dukkan fannoni, haka kuma, an gaggauta cimma burin tsara wuraren inda wadannan filaye da dakuna suka zauna.

"Yayin da aka zabi wuraren inda aka shirya giggina filaye da dakunan wasannin Olmpics na Beijing," a cewar Mr. Zhang, "akwai ka'idoji guda uku da aka bi, wato na farko dai, an kokarta yin amfani da albarkatu iri-iri, da yin tsimin albarkatun kasa, da takaita yawan mazauna wuraren wadanda suka yi kaura. Na biyu kuma shi ne, an himmatu wajen giggina wadannan filaye da dakuna a yankunan karkara na Beijing, inda ba a samu mazauna masu tarin yawa ba. Na uku wato na karshe shi ne, an giggina wadannan filaye da dakuna na wasannin Olympics bisa la'akari da surar tsohon gari da harkokin kiyaye abubuwan tarihi masu daraja."(Murtala)