Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-20 14:17:38    
Kantuna da dama masu sayar da abubuwan nan sun fito a birnin Beijing

cri

A cikin 'yan shekarun baya, a nan birnin Beijing, an yi ta kara sha'awar tufafi da abubuwan ado daga kasashen India da Pakistan da Nepal da dai sauran kasashen kudancin Asiya. Sabo da haka, kantuna da dama masu sayar da abubuwan nan sun fito a birnin Beijing. To, a cikin shirinmu na yau, za mu zaga da ku a wadannan kantuna.

A wurin da ke arewa da fadar sarakuna ta Beijing, akwai wani kyakkyawan tabki mai suna Shichahai, inda wani dan kabilar Tibet mai suna Luosang ke gudanar da wani kanti mai suna "kayayyakin aljanna" inda ake sayar da abubuwan ado na kudancin Asiya.

Wata rana, wakilinmu ya kai ziyara a wannan kanti. Tun daga gabar tabkin ne a iya hangen kofar kantin mai ban sha'awa, inda aka rataya wani farin labule mai hotunan giwa da dawisu masu lanuka iri iri. Da zarar aka shiga kantin, sai launuka iri daban daban ya jawo hankalinmu. An rataya darduma masu launuka iri iri a ko wane bango, a silin ma, an shimfida wani yadin rokon alheri. Ban da wannan, an ajiye kyawawan kayayyakin surfani da mayafi iri iri a kan tebur. Kayayyakin ado na azurfa ma sun kara daukar hankulan mutane a gaban gasun dawisu masu launin kore shar da fararen tsakuwoyi. Bayan haka kuma, ga kamshi da kide-kide irin na kabilar Tibet.

Mai kantin Luosang yana da bakar fata irin na 'yan kabilar Tibet, sa'an nan kuma, shi mutum ne mai zafin nama. Bayan da ya ji abin da ya kawo wakilinmu, sai ya nuna gaishe-gaishe ga masu sauraro da harshen Tibet, ya ce, 'Assalamu Alaikum, jama'a masu sauraro. Ni ne Luosang daga kantin kayayyakin aljanna, wanda wani dakin nune-nune ne daga Tibet. Ina yi muku fatan alheri.'

Iyalin Luosang ya yi suna ne a jihar Tibet wajen kera abubuwan ado na azurfa. A shekaru 7 da suka wuce, Luosang ya kafa wani kanti a Beijing, don sayar da abubuwan ado na Tibet. Luosang ya ce, Tibet na da tsayi, sabo da haka, tana kusa da sama, kuma mutanen Tibet suna bin addinin Buddah, ga shi kuma kayayyakin azurfa na Tibet suna da matukar kyaun gani, tamkar an same su ne daga aljanna, shi ya sa ya bai wa kantinsa suna 'kayayyakin aljanna'. Daga baya, ya kafa wani kanti daban don sayar da kayayyakin ado na India da Nepal.

Luosang ya ce, 'sabo da bunkasuwar yawon shakatawa, yanzu an yi ta kara zuwa India da Nepal, haka kuma an yi ta kara samun bayanai dangane da wuraren. Matasa na yanzu suna neman 'yanci, kuma ana ganin India da Nepal kasashe ne masu bin addnin Buddah, inda za a sami sanyaya rai. Kuma yawancin kayayyakin wurin ake samun su daya kawai, ba damar a sami daya daban, domin ana son nuna halinsu na musamman.

Miss Wei wata abokiyar ciniki ce a kantin Luosang. Ta bayyana cewa, 'Ina ganin tufafi da abubuwan ado daga kudancin Asiya suna iya biya wa mutane bukatu a fannoni daban daban. Ga su nan launuka iri iri, baki da shudi da ja da rawaya da dai sauransu, duka kana iya samunsu a cikin wadannan tufafi da abubuwan ado. In kana son abubuwa masu kyau da inganci, akwai su; ko kuma kana son sabbi ko tsoffi, to su za ka iya samu a kantin.

A wani kanti daban mai suna 'aljanna.ido' da ke cibiyar kasuwanci ta Beijing, wata kyakkyawar mata tana sayar da abubuwan ado masu ban sha'awa na kasar India. Ita ce mai kantin, sunanta Xu Manli. Ta fara gudanar da wannan kanti ne bayan da ta dawo daga yawon shakatawa a Tibet. Ta bayyana cewa, ana sayar da tufafi da abubuwan ado na Nepal da India da kuma na Pakistan a kantinta, ta kuma kafa wasu rassan kantinta a birnin Shanghai da Shenzheng da Chengdu na kasar Sin. Amma ko wane reshen kantin ya bambanta da juna, ko wane na da tsari nasa. Xu Manli ta ce, "Ina ganin abubuwan nan sun bayyana al'adun da addinin kasashen India da Pakistan sosai. Al'adun India da Pakistan suna da ban sha'awa, tare kuma da addinin kasashen da kuma tufafi da kayayyakin ado, ina tsammani ko wace yarinya za ta yi sha'awarsu ainun."

Akwai kuma sauran kantuna masu sayar da kayayyakin kudancin Asiya da dama, ba dai kawai sun biya bukatan matasa na neman kyaun gani da sabon salo ba, har ma sun kusantar da mutanen Sin da wadannan kasashe masu nisa da al'adunsu.