Masu sauraro, za a yi gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta shekarar 2008 a birnin Beijing ba da dadewa ba, gasar wasannin Olympic ta nakasassu ita ce gaggarumin biki na nakasassu na duniya baki daya. Ko shakka babu, shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu a kasar Sin zai kara ingiza bunkasuwar sha`anin nakasassu na kasar Sin. Yanzu, birnin Beijing yana sanya matukar kokarin aikin horo daga dukkan fannoni domin shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu lami lafiya. A cikin shirinmu na yau, bari mu kawo muku bayani kan wannan.
Saboda aikin hidima na gasar wasannin Olympic ta nakasassu yana da bukatun musamman, shi ya sa dole ne a mai da hankali kan aikin horo. Kwanakin baya ba da dadewa ba, karamar kungiyar sulhuntawa ta aikin horo ta gasar wasannin Olympic ta Beijing ta yi taron aikin horo na gasar wasannin Olympic ta nakasassu, inda shugaban kungiyar Zhu Shanlu ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympic ta nakasassu tana da tsarin musamman, domin biyan bukatun musamman na `yan wasa nakasassu, dole ne a yi wa masu aikin hidima na gasar wasannin Olympic ta nakasassu horo daga dukkan fannoni. Zhu Shanlu ya kara da cewa, aikin horon gasar wasannin Olympic ta nakasassu yana da ma`aunin sana`a, a sa`i daya kuma yana da wani tsarin musamman wato ya fi kyau dukkan jama`ar kasa su nuna biyayya da kulawa ga nakasassu. Ana iya ganin wannan daga fannoni hudu. `Da farko dai, aikin horon gasar wasannin Olympic ta nakasassu yana da harsashin al`adu mai zurfi; na biyu, yana da wuya; na uku, yana da ma`aunin sana`a na musamman; na hudu, ya danganta duk zamantakewar al`umma baki daya. Muna fatan nakasassu su kara samun biyayya da kulawa.`
Zhu Shanlu ya ce, yayin da ake gudanar da aikin horon gasar wasannin Olympic, abu mafi muhimmanci shi ne kara kyautata aikin hidima ga `yan wasa nakasassu, wato kamata ya yi a kara kyautata hadadden ingancin masu shirya gasar. Domin cim ma burin, dole ne a horar da jami`ai da masu aiki da kuma masu sa kai na gasar wasannin Olympic ta nakasassu.
A farkon watan Janairu na bana, sashen kula da masu sa kai na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya fara gudanar da ajin horar da malaman koyar da masu sa kai na gasar wasannin Olympic ta nakasassu a karo na biyu a sansanin atisayen motsa jiki na nakasassu na kasar Sin. Idan `yan takarar malaman koyar da masu sa kai sun ci jarrabawar da za a shirya musu, za su samu iznin zama malaman horar da masu sa kai na gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing.
Masu sa kai suna koyon ilmomi daban daban dake shafar wasannin Olympic na nakasassu, wadda a ciki, fasahar taimakon nakasassu ta fi muhimmanci, alal misali, tura kujerar nakasassu da takalma masu taya. Masu sa kai sun nuna kwazo da himma sun yi atisaye. Wani mai aikin sa kai Zhang Qian ya ce : `A ganina, bayan horo, na samu ilmin da abin ya shafa, kuma na sarrafa fasahar taimakon nakasassu, na sami ci gaba cikin sauri.`
Zhu Shanlu ya ce, nan gaba za a kara karfafa aikin taimakon nakasassu a Beijing baki daya. Ya ce: `Za a gudanar da aikin taimakon nakasassu tare da aikin farfaganda, a kai a kai ne za a kara aikin horon taimakon nakasassu a fannoni daban daban, alal misali a filin jirgin sama da dakin cin abinci da sauransu.
Zhu Shanlu yana ganin cewa, matsayin malaman horar da masu sa kai zai kawo tasiri ga ingancin aikin horo kai tsaye, shi ya sa kamata ya yi a mai da hankali kan wannan. Ya ce : `Ya fi kyau a zabi masu aikin kula da nakasassu da masanan motsa jiki na nakasassu da su zama malaman koyar da masu sa kai.`
Ban da wannan kuma, karamar kungiyar sulhuntawa ta aikin horo ta gasar wasannin Olympic ta Beijing ta buga wasu littattafan horon gasar wasannin Olympic ta nakasassu a jere, ta haka, za a gudanar da aikin horo yadda ya kamata. (Jamila Zhou)
|