
Masu karatu, a kafar babban dutse na Cuiweishan a yammacin birnin Beijing, akwai wani filin wasan harbi mai kyan gani. Shi ne filin wasan harbi na Beijing. Tun bayan kafuwarsa a shekarar 1955, kullum kungiyar wasan harbi ta kasar Sin ta mayar da shi a matsayin muhimmin sansanin aikin horaswa. Dimbin 'yan wasa gwanaye sun bullo a kan dandamalin ba da lambar yabo na gasar wasannin Olympic daga wannan filin wasa. A wannan shekara, za a yi shirye-shiryen wasan harbin faifai da sauri a gasar wasannin Olympic ta Beijing a filin wasan harbi na Beijing. 'Yan wasa masu yawa daga wurare daban daban na duniya za su taru a nan, za su yi takara mai tsanani a nan, inda zakarun gasar wasannin Olympic da ba a iya kidaya yawansu ba suka taba samun aikin horaswa.
Sashen wasan harbin faifai da sauri na cikin yammacin filin wasan harbi na Beijing. Fadinsa ya kai misalin murabba'in mita 6170. A lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing, zai karbi 'yan kallo kimanin dubu 5. A matsayinsa na filin wasa da aka yi masa kwaskwarima da kuma fadada shi, an fara sabuntawa da kuma ajiye na'urorin zamani a cikinsa tun daga ran 24 ga watan Maris na shekarar 2006. Kuma an kammala dukkan ayyuka a watan Agusta na shekarar bara. A gaskiya dai, ba a gamu da matsala ba a harkokin kwaskwarima. Amma a farkon lokacin da aka kaddamar da ayyukan, wani lamari ya girgiza masu yin kwaskwarima.
1 2
|