Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-19 15:15:16    
Birnin Hangzhou na kasar Sin yana yin kokari wajen bai wa jama'a tabbaci ga samun jiyya mai inganci

cri

A farkon shekara ta 2006, Liu Jianxing, dan lardin Jiangxi da ke cin rani a birnin Hangzhou ya kamu da cutar fitsari. Domin ci gaba da rayuwarsa, dole ne a tace mummunan sinadaran da ke cikin jininsa sau biyu a ko wane mako, ta haka yawan kudaden da Mr. Liu ya kashe wajen samun jiyya ya kai a kalla kudin Sin Yuan dubu shida a ko wane wata. Ko shakka babu wannan kudin jiyya wata babbar jimla ce ga Mr. Liu da matarsa wadanda yawan kudaden shiga da suke samu ya kai Yuan 3000 kawai a ko wane wata. Amma abin sa'a shi ne bisa wata sabuwar manufar da birnin Hangzhou ya bayar ba da jimawa ba, muddin Mr. Liu ya ba da kudin Yuan 100 kawai a ko wane wata, to, zai iya shiga inshorar jiyya wajen warkar da cututtuka masu tsanani kamar yadda mazauna birnin ke yi. Kuma Mr. Liu ya bayyana cewa,

"In babu inshorar jiyya, to ban san me zan yi ba, kamar duniya ta fadi a kaina. Haka kuma in ban shiga inshorar jiyya ba, ko kusa ba na da kudin ganin likita."

A shekara ta 2001, an shigad da dukkan ma'aikatan gwamnati da kuma kamfanoni na birnin Hangzhou da kuma gundumominsa cikin inshorar jiyya. Amma kafin shekera ta 2007, masu ci rani da suka zo daga sauran lardunan kasar Sin kamar Liu Jianxing da kuma yaransu, har ma wasu tsoffi ba su samu tabbaci wajen samun jiyya ba, kuma kullum su kan shiga mawuyacin hali sakamakon rashin samun isassun kudaden jiyya.

Madam Zhao Caiyun da shekarunta ya kai 71 da haihuwa ta je birnin Hangzhou ne tare da mijinta bayan da ta yi ritaya daga wani kamfani na lardin Liaoning da ke arewa maso gabashin kasar Sin yau da shekaru fiye da 20 da suka gabata. Domin ba ta samu shiga inshorar jiyya ba, shi ya sa ba ta samu ko kwabo da ta kashe wajen ganin likita wanda ake iya mayar mata ba. Sabo da haka ko da yake tana kamuwa da cutar data, amma ba ta je asibiti don ganin likita ba. Kuma ta gaya mana cewa,

"Na kamu da cutar data har shekaru fiye da goma, amma kullum na kan sha magunguna kawai domin sassauta zafinta. Amma a wannan karo, na ji zafi kwarai da gaske, kuma ban iya jurewa ba, ba yadda za a yi sai na shiga asibiti. Amma abin sa'a shi ne, yanzu na riga na shiga ishorar jiyya wajen warkar da cututtuka masu tsanani."

Inshorar jiyya wajen warkar da cututtuka masu tsanani da Madam Zhao ta ambata a baya ita ce wadda aka samar don mazauna tsofaffi na birnin Hangzhou daga ran 1 ga watan Afril na shekara ta 2007, dukkan mazauna tsofaffi na birnin da ba su shiga babbar inshorar jiyya ta birane da gundumomi ba suna iya shiga inshorar.

Haka kuma bisa abubuwan da aka tanada a cikin inshorar, an ce, lokacin da Zhao Caiyun ta fito daga asibiti, inshorar ta mayar mata kudin jiyya Yuan dubu 9 daga cikin kudade fiye da dubu 24 da ta kashe. Ta haka lalle tsarin ba da tabbaci ga samun jiyya ya kawo wa fararen hula alheri na a zo a gani.

Furofesa Yang Jianxin na cibiyar binciken kimiyyar zaman al'umma ta lardin Zhejiang yana ganin cewa, aiwatar da wadannan manufofi wani muhimmin mataki ne domin jama'a wadanda suke iya more sakamakon da kasar Sin ta samu wajen bunkasuwa bisa shiri. Kuma ya kara da cewa,

"haka kuma wannan ya bayyana wani muhimmin ra'ayin birnin Hangzhou wajen raya wani birnin da ke da ingancin zaman rayuwar jama'a, wato jama'a na iya more sakamakon da aka samu wajen bunkasuwa, kuma mun raya birnin ne domin jama'a. Warware matsalolin zaman rayuwa na fararen hula hakki mafi muhimminci ne na gwamnati. "(Kande Gao)