Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-18 15:14:34    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri
---- Kwanan baya a babban dakin taruwar jama'a, an kira taron shan shayi na mutane 'yan kabilu daban-daban domin maraba da sallar bazara, mutane 'yan kabilu daban-daban na birnin Beijing wadanda yawansu ya wuce 1,000 sun taru gu daya cikin farin ciki domin murnar sallar bazara.

A gun taron, a madadin kwamitin kabilu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da kwamitin kula da harkokin kabilu na kasa da kuma kwamitin kabilu da addinai na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasa ne, Mr. Redi, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya yi wa jama'ar kabilu daban-daban na duk kasa baki daya barka da salla da yi musu kyakkyawan fatan alheri.

Mr. Redi ya ce, shekarar 2007 wata shekara ce da aka samu ci gaba sannu a hankali wajen harkokin hadin kai da bunkasuwa na kabilun kasar Sin. Gwamnatin kasar tana mai da muhimmanci sosai kan harkokin kabilu, kuma ta sa lura sosai ga ci gaban da aka samu a wuraren kananan kabilu, kuma ta dauki manyan matakai a jere domin wannan aiki. Ya nanata cewa, shekarar 2008 shekara ta farko ce wajen gudanar da manufofin manyan tsare-tsare da aka tsayar a gun babban taron wakilai na 17 na J.K.S. daga duk fannoni, yana fatan dukkan mutane za su shiga babban sha'anin samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya da raya zaman al'umma mai jituwa, kuma za su samun sabbin nasarori cikin yunkurin tarihi na raya zaman al'umma mai wadata daga duk fannoni, da raya zaman gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, ta yadda za su bude sabon zamani domin harkokin hadin kai da samun ci gaba na kabilun kasar Sin.

---- Jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin tana tsayawa kan bunkasa sana'o'i masu sigogi musamman, ta yadda wadannan sana'o'i suna ta zama muhimmin karfin makamashi wajen samun babban ci gaban a jihar.

Mun samu labari cewa, cikin shekaru 5 da suka wuce, jihar Tibet ta ware kudin Sin fiye da Yuan biliyan 1 domin ba da taimako ga bunkasa ayyuka noma da makiyaya fiye da 170, ana nan ana kara lamirin manoma da makiyaya a fannin hajjoji da kasuwanni da yi gasa. Kuma an samu ci gaba da sauri wajen sana'o'in likitanci da yin magungunan Tibet, da samar da abinci mai inganci, da kuma sana'o'in hannu. Ban da wannan kuma jihar Tibet ta rubanya kokari wajen bunkasa sana'ar yawon shakatawa, yawan mutane masu yawon shakatawa da jihar nan ta karba a shekarar da ta wuce daga cikin kasar da kuma kasashen waje ya kai miliyan 4 da dubu 20, yawan kudin Sin da aka samu daga wajen sana'ar yawon shakatawa kuma ya riga ya kai kashi 14 cikin 100 bisa na jimlar kudin da aka samu daga aikin kawo albarkar jihar.(Umaru)