Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-18 14:06:38    
An farfado da ayyukan sake gina wuraren da bala'in ya shafa a kudancin kasar Sin cikin armashi

cri

Ana farfado da ayyukan sake gina wuraren da bala'in ya shafa a kudancin kasar Sin daga dukkan fannoni cikin armashi.

Lardin Hunan yana kokarin gyara layukan kananan wutar lantarki da ruwan pmpo da suka lalace, don su yi kokari kafin karshen watan Maris, za a sake farfado da samar da wutar lantarki yadda ya kamata. Hukumar banki ta lardin Hunan ta riga ta samar da rancen kudin agaji fiye da Yuan biliyan 7 wajen taimaka wa wuraren da bala'in ya shafa da kuma nuna goyon baya ga ayyukan sake gina wuraren da bala'in ya shafa.

Birnin Guilin da ke lardin Guang Xi, mashahurin birnin ne a fannin yawon shakatawa a duniya, yanzu yana kokarin gadan-gadan wajen sake gina ayyukan tushe da suka lalace a wurin, kuma za su dauki matakai wajen gudanar da ayyukan sake gina wuraren da bala'in ya shafa.

A lardin Jiangxi, an riga an kebe kudin agaji da yawansu ya kai Yuan biliyan 1.5 wajen yaki da bala'in da kuma taimaka wa mutanen da bala'in ya shafa da farfado da sha'anin noma da gandun daji da 'ya'yan itatuwa yadda ya kamata.

Kwanakin nan, ma'aikata masu aikin gyaran wutar lantarki fiye da dubu 4 da aka dauke su daga sauran lardunan Sin cikin gaggawa, yanzu suna taimaka wa lardin Zhejiang wajen kaddamar da ayyukan yaki da dusar kankara da kuma farfado da wutar lantarki.

Ya zuwa ran 17 da karfe 5 da yamma, hanyoyin jiragen kasa da babbar hanyar sun riga sun kama aiki yadda ya kamata, hukumar kula da jiragen kasa da ma'aikatar zirga-zirga ta kasar Sin za su ci gaba da jigilar kwal da wutar lantarki. A kasuwannin da ke wuraren da bala'in ya shafa, ana ci gaba da samar da kayayyaki cikin kwanciyar hankali.(Bako)