Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-16 18:39:00    
Bai kamata hukumar kula da wasannin Olympics ta duniya ta dauki nauyin daidaita matsalar duniya ba, in ji Jacques Rogge

cri
A yayin da yake hira da wakilin wani gidan telebijin kasar Faransa a jiya 15 ga wata, Jacques Rogge, shugaban hukumar kula da wasannin Olympics ta duniya, ya bayyana cewa, hukumar kula da wasannin Olympics ta duniya hukuma ce ta wasanni, ba ta siyasa ba, shi ya sa bai kamata ta taka rawar siyasa ba wajen daidaita matsalar duniya.

A lokacin hirar, Mr.Rogge ya ce, ba ya damuwa da kaurace wa wasannin Olympics na Beijing da za a iya yi, "sabo da masu kaurace wa wasannin za su jawo wa kansu hukunci ne kawai". Rashin hallara a gun wasannin Olympics da wasu za su yi "ba zai lalata wasannin ba."

Mr.Rogge ya kuma kara da cewa, idan 'yan wasa sun yi amfani da wasannin Olympics a matsayin fagen siyasa, za su sami hukunci."

Game da hada batun Darfur na Sudan da wasannin Olympics, har ma kaurace wa wasannin, da wasu suka yi, shugaba Bush na kasar Amurka ya yi hira da wakilin BBC a kwanan baya cewa, zai halarci wasannin Olympics na Beijing kamar yadda ya shirya. Ya ce, wasannin Olympics wasanni ne, kuma ba zai tattauna batun siyasa ba bisa wasan.(Lubabatu)