Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-15 16:32:37    
'Yancin kai a yayin da manyan kasashe suke kara tsananin takarar da ke tsakaninsu

cri
Kwanan nan, halin da shiyyar Kosovo ta Serbia wadda Majalisar Dinkin duniya ke daukan nauyin aiwatar da harkokinta bisa wuyanta take ciki na neman 'yancin kai ya haifar da sabon abu. Bisa labarin da abin ya shafa, an bayyana cewa, mai yiyuwa ne Kosovo za ta yi shelar samun'yancin kai a ranar 17 ga watan da muke ciki. Bisa halin nan, bisa rokon da Serbia ta yi masa, Kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya zai kira taron gaggawa a ranar 14 ga wannan wata kan halin da Kosovo ke ciki, a sa'I daya kuma, takarar da ke tsakanin bangarori daban daban kan batun Kosovo ita ma ta kara tsanani.

Bisa matsayin wani lardin da ke aiwatar da harkokinsa na kansa na Jamhuriyar Serbia ta kawancen tarayyar Yogoslaviya, makircin neman 'yancin kan Kosovo ya gamu da adawa sosai da Serbia da Rasha suka yi. Amma, dayake kasar Amurka da kawancen tarayyar kasashen Turai suna nuna goyon bayansu, shi ya sa takin da ake dosawa gaba don neman samun 'yancin kan Kosovo sai kara sauri yake yi a kowace rana. Direktan cibiyar yin nazari kan batutuwan kawancen tarayyar Turai ta kasar Sin Mr Xing Hua ya bayyana cewa, dayake an riga an sami goyon baya daga kasar Amurka da kawancen tarayyar kasashen Turai a kan batun neman 'yancin kan Kosovo, shi ya sa ba a iya kawar da al'amarin shelar samun 'yancin kan Kosovo ba, abu ne da zai faru ba shakka, wato tun da wurwuri ko tun da dadewa .

 Kosovo ta kasance wuri ne da kabilu da yawa suke zama a cunkushe. Tun daga shekaru 90 na karnin da ya shige har zuwa yanzu, kabilar Albaniya ma da yawansu ya kai kashi 90 cikin dari bisa yawan mutanen wurin suna ta neman 'yancin kai, amma sun sami kiyayya daga gwamnatin Serbia. A shekarar 1999, kasar Amurka ta tayar da yakin Kosovo, bayan haka, Majalisar dinkin duniya ta soma daukar nauyin aiwatar da harkokin Kosovo bisa wuyanta, kuma an kafa  kwarya-kwaryar gwamnati mai aiwatar da harkokinta na kanta. A karshen shekarar 2005, gwamnatin Searbia da hukumar kabilar Albaniya ta Kosovo sun soma yin shawarwari a tsakaninsu a kan matsayin karshe na Kosovo, amma ba a sami kowane ci gaba ba. Bayan shawarwarin karshe da aka yi a karshen shekarar bara, ba sau daya ba ba sau biyu ba hukumar Kosovo ta bayyana cewa, ba za ta shiga shawarwarin da za a yi ba, a akasin haka za ta yi shelar samun 'yancin kan Kosovo ita kadai. Bisa albarkacin kusancin samun 'yancin kan Kosovo, sai kasar Amurka da Rasha da kungiyar tarayyar kasashen Turai suna kara karfin takara a tsakaninsu.

A ranar 13 ga wannan wata, kakakin fadar shugaban kasar Amurka Madam Perino ta bayyana cewa, ya kamata Kosovo tana ci gaba da tinkara zuwa samun 'yancin kai, kuma ya kamata gamayyar kasa da kasa su nuna goyon bayansu. Game da wannan , wani mai bincike na cibiyar yin nazari kan batutuwan zamantakewar al'umma ta kasar Sin Mr Jiang Yi ya bayyana cewa, bayan kammala yakin cacar baki. Kasar Amurka da sauran kasashen Yamma kullum suna son mayar da shiyyar Balkans don ta zama sansaninsu a karkashin sararfawarsu. Batun da aka yi na cewar wai kawar da rikici da kuma kawar da babban dalilin da ya haifar da rikicin shi ne kirarin da kasashen yamma ciki har da kasar Amurkan suka yi bisa dabararsu ta kansu. Amma babban makasudinsu shi ne don mayar da shiyyar don ta zama sansanin kasashen yamma. Game da wannan Mr Xing Hua ya bayyana cewa, tun lokacin da, kungiyar tarayyar kasashen Turai suka rike da ra'ayinsu na nuna shakka a kan batun neman 'yancin kan Kosovo, su ma sun yi damuwa da samun sauran al'amuran da suka yi daidai da batun Balkans. Amma a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kungiyar tarayyar kasashen Turai tana bayyana cewa, idan ba a iya daidaita batun kabilar Albaniya na nacewa ga neman samun 'yancin kan Kosovo ba, to suna damuwa da cewa, mai yiyuwa ne shugabannin kabilar Arbaniya za su dauki matakin nuna karfin tuwo, in hakan ya faru, za a kawo hargitsi a shiyyar Kosovo, har a duk shiyyar Balkans. Amma, a cikin kungiyar tarayyar kasashen Turai, wasu kasashe har wa yau dai sun bayyana cewa, ba za su amince da shelar da za a yi ta samun 'yancin Kan Kosovo ba.

Ra'ayin kasar Sin shi ne, ya kamata a daidaita batun Kosovo a karkashin shugabancin Majalisar Dinkin duniya.(Halima)