Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-15 16:26:52    
Tarihin gidan rediyon kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Mohammed Idi Gargajiga, shugaban Gombawa CRI Listeners Club, wanda ya zo daga jihar Gombe, tarayyar Nijeriya. Kwanan baya, malam Mohammed ya turo mana wata wasika, inda ya yi mana dimbin tambayoyi game da tarihin gidan rediyon kasar Sin, ciki har da shin gidan rediyon kasar Sin baki daya na da yawan ma'aikata nawa? nawa ne ma'aikata baki da suka zo daga kasashen waje? ko gidan rediyon kasar Sin yana da kungiyoyi ko club-club na masu sauraronsa da suka fito daga kasashen duniya?da dai sauransu. Sabo da haka, masu sauraro, yanzu sai ku gyara zama ku sha wani bayani dangane da gidan rediyon kasar Sin.

Gidan rediyon kasar Sin, wato China Rediyon International, ko kuma CRI a takaice, an kafa shi ne a ranar 3 ga watan Disamba na shekarar 1941, kuma shi gidan rediyo ne da ke watsa shirye-shiryensa ga kasashen duniya baki daya. Manufar gidan rediyon kasar Sin shi ne "fadakar da duniya a kan Sin da fadakar kasashen duniya a kan duniya da kuma karfafa fahimtar juna da dankon zumunci a tsakanin jama'ar kasar Sin da na duniya."

A yanzu haka dai, gidan rediyon kasar Sin na watsa shirye-shiryensa cikin harsuna 43, ciki har da harsunan waje 38 tare kuma da daidaitaccen Sinanci da kuma sauran yaren Sinanci 4. Ya zuwa karshen shekarar 2006, gaba daya ne gidan rediyon kasar Sin na gabatar da shirye-shiryensa fiye da awa 1100 a kowace rana.

Bayan haka, gidan rediyon kasar Sin ya kuma bude tashoshinsa a kasashen waje. A ranar 27 ga watan Faburairu na shekarar 2006, gidan rediyon kasar Sin ya bude tasharsa ta farko a ketare, wato FM 91.5 da ya bude a birnin Nairobi, babban birnin kasar Kenya. Sa'an nan, a ran 19 ga watan Nuwamba na shekarar 2006, gidan rediyon kasar Sin ya bude tasharsa ta FM 93 a birnin Vientiane, babban birnin kasar Laos. Daga bisani, ya kuma bude tasharsa ta FM a birnin Yamai, babban birnin jamhuriyar Nijer, wato a kan FM 106. Ya zuwa yanzu dai, gidan rediyon kasar Sin ya riga ya kafa tashoshinsa 11 a kasashen waje, a yayin da yake kuma hada kansa da gidajen rediyo na ketare 149.

Sai kuma a fannin internet, tashar internet ta gidan rediyon kasar Sin, wato CRIonline wata muhimmiyar tashar internet ce a kasar Sin, a halin yanzu dai, tashar na da shafunan da ke amfani da rubutun harsuna 43 da kuma muryar harsuna 48. Jama'a na kasashe da shiyyoyi fiye da 160 a duniya su kan karanta bayanai daga tashar, kuma a kowace rana, mutane kimanin dubu 700 suna sauraron shirye-shiryensa daga tashar. Masu sauraro, ko da yaushe, duk inda kuke, kuna iya karanta labarai da dumi-duminsu da kuma shakatawa da shirye-shirye masu kayatarwa, idan kun kama tasharmu ta internet, kada ku manta, adireshinmu na internet shi ne www.cri.cn.

Bayan haka, gidan rediyon kasar Sin yana kuma gudanar da jaridu da kuma mujalloli. Jaridar labaran duniya da yake gudanarwa na ba da labaran duniya da ke shafar siyasa da tattalin arziki da al'adu da wasanni da ilmi da kimiyya da zaman al'umma da dai sauransu, kuma yana gudanar da mujalloli 39 cikin harsunan waje, wadanda ke samun masu karatu a kasashe daban daban.

Domin samo labaran abubuwan da ke faruwa a ko ina a duniya da dumi duminsu, gidan rediyon kasar Sin ya kuma bude ofishoshin wakilansa guda 30 a muhimman kasashe da shiyyoyin duniya, kuma ofishinmu a birnin Lagos, tarayyar Nijeriya na daya daga cikinsu.

Masu sauraro, mun dai bayyana muku harkokin da gidan rediyon kasar Sin ke gudanarwa, kuma ma'aikatan rediyon kasar Sin kusan 2000 tare kuma da ma'aitansa baki 130 da suka zo daga kasashe daban daban su ne suke gudanar da harkokin. Kamar a sashen Hausa, yanzu akwai ma'aikata Sinawa 13 da kuma masana baki 3.

Sabo da kokarin da ya yi, gidan rediyon kasar Sin ya sami karbuwa daga masu sauraronsa a duniya, kuma yanzu yana samun kungiyoyi ko kulob-kulob fiye da 3600 na masu sauraronsa da suka zo daga kasashen duniya daban daban. (Lubabatu)