Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-15 16:03:39    
Mazauna fiye da 800 na kwarin kogin Yili na jihar Xinjiang sun sha bala'in kankara

cri
Sakamakon sauye-sauyen yanayi shi ya sa bala'in kankara da ake fama da shi a kwarin kogin Yili na jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin ya kara tsanani, zuwa ran 12 ga wata da akwai mazauna da yawansu ya kai fiye da 800 na wannan wuri da suke fama da bala'in.

An ce, bayan bala'in ya auku, nan da nan shugabannin wurin suka shugabanci jami'an hukumomin kula da harkokin jama'a da na ayyukan tsare ruwa don su shirya mutane kuma sun doshi wuraren bala'in don aikin ceto. Yanzu an riga an tsugunar da mutane masu fama da bala'in yadda ya kamata, ba wanda ya mutu ko ya ji rauni sakamakon bala'in. (Umaru)