Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-14 19:01:27    
Jihar Xinjiang ta dauki matakai don taimakawa 'yan kananan kabilu wajen samun aikin yi

cri

Jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur tana arewa maso yammacin kasar Sin, 'yan kananan kabilu da yawa suna zama a jihar, akwai kananan kabilu 46 a birnin Urumqi daya kawai. Amma, saboda dalilai da yawa, ba a sa san alheri kan halin samun aikin yi na 'yan kananan kabilun da ke zama a wurin. A 'yan shekarun da suka wuce, gwamnatin birnin Urumqi ta dauki matakai da dama kan matsalar, kuma ta samu nasara sosai. A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan wannan.

Gundumar Tianshan tana karkashin jagorancin gwamnatin birnin Urumqi kai tsaye, 'yan kananan kabilu kashi daya cikin hudu bisa na dukkan birnin suna zama a gundumar. Saboda dalilai da dama, ciki har da harsuna, samun aikin yi na kananan kabilu ya zama wata babbar matsalar da ake fuskanta. Mr. Wang Long, daraktan cibiyar kula da harkokin sake samun aikin yi ta gundumar Tian shan, ya gabatar da cewa, "Yana da wuya a fannin samun aikin yi na 'yan kananan kabilu. A waje daya, yawancin 'yan kananan kabilu suna iya harshen kabilarsu kawai, amma ya kasance da kabilu daban daban a birnin Urumqi, ciki har da kabilun Han, da Uygur, da kuma Khazak, da dai sauransu, saboda haka, a kan yi amfani da harshen yau da kullum, wato harshen Han a birnin. Na biyu, wasu 'yan kananan kabilu ba su taba karbar limi ba."

Kan wannan halin da ake ciki, hukumomin da abin ya shafa na gwamnatin gundumar Tianshan, sun mai da samun aikin yi na kananan kalibu kan muhimmin matsayi, kuma sun mai da hankulansu kan kara bayar da ilmin fasaha. Suna gudanar da ayyukan ba da ilmin fasaha a fannoni daban daban kan halin da kananan kabilu daban daban ke ciki. Bisa kididdigar da aka yi an ce, tun bayan da aka soma aiwatar da wannan mataki, 'yan kananan kabilu kusan 3100 sun samun aikin yi a farkon watanni 11 na shekarar 2007 kawai, wadanda suka samu aikin yi ta hanyar karbar ilmin fasaha sun kai kusan 1900. Hasiyet, wata yariniyar kabilar Uygur tana daya daga cikinsu.

Hasiyet tana zama a gundumar Tianshan, ba ta samu aikin yi ba tun bayan da ta gama karatunta a sakandare. Daga baya kuma, bisa sha'awar kanta, ta karbi ilmin fasahar dinki har watanni 6, a farkon shekarar bara, ta samun aikin dinki a karkashin taimako daga cibiyar kwadago da jin dadin jama'a ta wurin. Tun daga lokacin, ba za ta rinka dogaro a kan taimakon kudi daga gwamnati ba.

"Kullum ba na da aikin yi tun bayan da na gama karatu a sakandare, daga baya kuma, masu aiki na al'ummarmu sun zo gidana, don fahimtar halin da nake ciki, kuma na yi rajista don neman aikin yi. Bayan da na karbi ilmin fasahar dinki, sai na samu aikin yi. Lallai, yanzu ina jin dadin zama."

Gwamnatin gundumar Tianshan ta aiwatar da ayyukan ba da ilmin fasaha a fannoni fiye da goma, ban da abinci, da dinki, kuma akwai tukin motoci, da kamputa, da kuma ilmin akanta, da dai sauransu. Mr. Wang Long, daraktan cibiyar kula da harkokin sake samun aikin yi ta gundumar Tianshan ya bayyana cewa, bayan da aka kawo karshen ba da ilmin fasaha, al'ummar za ta taimaka wa masu karbar ilmi don su samun aikin yi cikin watanni uku.

"Mun shirya mutanen da suka rashin aikin yi zuwa makarantu, don samun ilmin fasaha bisa sha'awarsu. Bayan haka kuma, mun gabatar da damar samun aikin yi ga su."

Ba gundumar Tianshan kawai ba, kuma a sauran gundumomi na birnin Urumqi an tsara manufofi kamar irin nan bisa hakikanan halinsu.

Bugu da kari kuma, hukumar kwadago da jin dadin jama'a ta birnin Urumqi ta dauki matakai da dama, don taimaka wa 'yan kananan kabilu wajen samun aikin yi. Kamar misali, tana kara samar da sabbin guraban aikin yi, da kuma ba da tabbaci wajen bayar da sabbin aiki bisa gwargwado ga 'yan kananan kabilu." Shugaban hukumar kwadago da jin dadin jama'a madam Zhu Wenzhi ta ce, "Bunkasa tattalin arziki na kananan kabilu, ita ce hanyar kai tsaye ta kara samun aikin yi na kananan kabilu. Saboda haka, mun kara samar da guraban aikin yi ga 'yan kananan kabilu a wuraren yawon shakatawa, wadanda ke dacewa da bunkasuwar tattalin arziki ta kananan kabilu, da kuma jawo matafiya na kasashen ketare. A sakamakon haka, a lokacin da ake samun kudi da yawa wajen tattalin arziki, a waje daya kuma mun bayar da yawan guraben aikin yi ga 'yan kananan kabilu na birninmu."

Tare da tabbatar da wadannan matakai, tun daga shekarar 2001 har zuwa watan Nuvamba na shekarar 2007, 'yan kananan kabilu na birnin Urumqi da suka samu aikin yi, sun kai kusan dubu 72, wato sun kai kashi 23 cikin dari bisa na dukkan mutanen da suka samun aikin yi. Saboda haka, wadannan matakan da gwamnatin Urumqi ta dauka, sun samu karbuwa sosai a tsakanin 'yan kananan kabilu da ke neman aikin yi.