A cikin kwanakin nan, manazarta na kasar Amurka sun gano cewa, idan mata masu ciki suka kamu da ciwon sakamakon kiba fiye da kima, to mai yiyuwa ne yaransu za su gaji ciwon. Sakamakon haka a cikin shekarun nan da suka gabata, yawan jarirai masu kiba na kasar Amurka ya samu karuwa sosai.
Bisa labarin da muka samu a tashar Internet ta mujallar Nature ta kasar Birtaniya, an ce, bayan da manazarta na kwalejin ilmin likita na jami'ar Harvard ta kasar Amurka suka yi bincike, sun gano cewa, muhimmin dalilin da ya sa wasu yara suke da kiba fiye da kima shi ne sabo da nauyin jikin iyayensu mata ya karu sosai yayin da suke da ciki.
Akwai dalilai da yawa da suka haifar da wannan hali da ake ciki. A wasu lokuka, idan nauyin jikin mata masu ciki ya samu karuwa fiye da kima, to za su kamu da ciwon sukari sakamakon samun ciki, sabo da haka yawan sinadarin insulin da ke jikin jariransu zai karu, wanda zai sa jarirai su kara son cin abinci, ta haka sannu a hankali nauyin jikin jarirai ya kan karu fiye da kima. Ban da wannan kuma, nauyin jikin iyaye zai taka rawa ga nauyin jikin jariransu ta maniyyi da ovum.
Haka kuma nazarin ya bayyana cewa, abinci zai ba da tasiri ga nauyin jikin jarirai. Nauyin jikin jariran da aka ciyar da su da garin madara zai karu mafi sauri idan an kwatanta shi da wadanda suka sha nonon iyaye mata.
Domin yara suna iya samun lafiyar jiki, iyayensu mata su kan ba su kwarin gwiwa wajen cin abinci, amma bisa wani sakamakon nazari da kasar Amurka ta bayar, an ce, mai yiyuwa ne samun kiba fiye da kima ga yara yana da nasaba da hanyoyin cin abinci da su kan bi bisa bukatar iyayensu mata.
Bisa labarin da mujallar ilmin likita na yara ta kasar Amurka ta bayar, an ce, manazarta na jami'ar Michigan ta kasar Amurka sun gudanar da wani bincike kan iyaye mata 71 da yaransu 71 wajen ci abinci daban daban iri hudu. Abinci iri biyu daga cikinsu su ne waina da soyayyen dankali da su kan ci a zaman yau da kullum, kuma abincin iri biyu daban su ne mooncake da soyayyun 'ya'yan itatuwa da kayan lambu wadanda ba safai a kan ci ba. Haka kuma a cikin wadannan iyaye mata, sulusi daga cikinsu suna da kiba fiye da kima, yayin da yaran da yawansu ya kai kusan kashi 12.5 cikin dari suna da kiba fiye da kima.
Sakamakon binciken ya bayyana cewa, ko da yake iyaye mata masu kiba ba su bai wa yaransu kwarin gwiwa wajen cin abinci sau da yawa idan an kwatanta shi da yadda iyaye mata wadanda ba su da jiki sosai suke yi, amma yaran iyaye mata masu kiba sun fi karbar shawararin iyayensu mata wajen cin abinci idan an kwatanta su da yara na iyaye mata da ba su da jiki sosai. Haka kuma ana iya ganin irin wannan bambanci a bayyane yayin da ake cin abincin ba safai a kan cin irinsa ba, kashi 67 cikin dari daga yaran iyaye mata masu kiba suna son cin irin wannan abinci bayan da iyayensu mata suka ba su kwarin gwiwa, amma wannan jimla ta kai kashi 52 cikin dari kawai ga yara na iyaye mata da ba su da jiki sosai.
Manazarta sun yi hasashen cewa, dalilin da ya sa yaran iyaye mata masu kiba suka fi karbar shawararin iyayensu shi ne wadannan yara sun fi son mayar da martani kan muhalli wajen cin abinci, haka kuma watakila sabo da shawarar da iyaye mata masu kiba suka bayar wajen cin abinci ta sha bamba da wadda iyaye mata da ba su da jiki sosai su kan yi. Bugu da kari kuma manazarta sun gano cewa, iyaye mata masu kiba wadanda yaransu ke da nauyin jiki sosai sun fi son ba wa yara kwarin gwiwa wajen ci abincin da ba su taba ci ba, kuma ba su son bai wa yara kwarin gwiwa wajen cin abincin da su kan ci. Sabo da haka manazarta suna ganin cewa, watakila iyaye mata masu kiba suna ganin cewa, akwai abubuwan gina jiki mafi yawa a cikin abincin da ba safai su kan ci irinsa ba.
|