Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-13 16:46:21    
Sin za ta kafa cibiyar musayar ikon dab'i ta duniya don bunkasa sana'ar dab'i

cri

Kwanan baya dai, cibiyar kiyaye ikon dab'i ta kasar Sin ta kuduri aniyar kafa wata cibiyar musayar ikon dab'i ta duniya a matsayin gwamnatin kasar a wata mai kamawa da zummar bunkasa sana'ar dab'i ta kasar Sin. Mr. Duan Guijian, daraktan cibiyar kiyaye ikon dab'i ta kasar Sin ya fada wa wakilinmu cewa : ' An yanke shawarar kafa wata cibiyar musayar ikon dab'i ta duniya a matsayin gwamnatin kasa ne domin biyan bukatun inganta sana'ar kirkiro hasashen al'adu. Wannan cibiya za ta yi hidimomi a muhimman fannoni hudu. Fanni na farko shi ne, yin hidima ga tabbatar da bayanai kan rajistar ikon dab'i ; Na biyu shi ne, yin hidima ga musayar ikon dab'i ; Na uku shi ne, yin hidima ga kare ikon dab'i ; Fanni na hudu wato na karshe shi ne, yin hidima ga goyon bayan da kwararru a fannin dab'i suke nunawa.'

Sa'annan Mr. Duan ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin na dukufa wajen raya wata kasa irin ta sabon salo yayin da take mai da hankali sosai kan kara samun karfin da take da shi na kirkire-kirkire cikin cin gashin kanta da kuma bunkasa sana'ar ikon mallakar ilimi, da kafa wata cibiyar musayar ikon dab'i a matsayin gwamnatin kasa.

Jama'a masu saurare, ko kuna sane da cewa, sana'ar ikon dab'i ta kasar Sin ta samu bunkasuwa da saurin gaske a 'yan shekarun baya. Yanzu, gwamnatin kasar Sin ta kara bude kofa ga kasashen waje domin yin tattaunawa da musanye-musanye da kuma hadin gwiwa tare da Gamayyar Kasa da Kasa a fannin ikon dab'. Kafin wannan dai, kasar Sin takan yi musayar ikon dab'i ne ta wasu cibiyoyi da hukumomin musayar ikon dab'i na wurare daban-daban na kasar. A lokaci guda, cibiyar kiyaye ikon dab'i ta kasar Sin ta samu nasarar gudanar da nune-nunen ikon dab'i na litattafai na duk kasa har sau uku. Hakan ya samar da wani muhimmin dandamali ga mawallafa da hukumomi masu amfani da littattafai iri daban-daban wajen musayar ikon dab'i. An labarta cewa, yanzu cibiyar kiyaye ikon dab'i ta kasar Sin tana yin hadin gwiwa sosai tare da gwamnatin unguwar Dongcheng ta birnin Beijing domin share fagen kafa cibiyar musanyar ikon dab'i ta duniya. Mataimakin shugaban unguwar Dongcheng Mr. Wang Peili ya furta cewa: " Shirin kafa cibiyar musayar ikon dab'I ta duniya ya samu goyon baya daga hukumar kula da harkokin ikon dab'I ta kasar Sin da kuma gwamnatin birnin Beijing. Hakikanin makasudin aikinmu shi ne, kafa wata cibiya bada labarai da ta fi samun kwarjini a dukkan fadin kasar dangane da aikin rajistar ikon dab'I da kuma na amince da shi,da kafa wata kasuwar musayar ikon dab'I a matsayin gwamnatin kasa da kuma kafa wani dandamalin duk kasa na gudanar da harkokin jari na ikon dab'I".

Bisa labarin da muka samu, an ce, za a kafa cibiyar musayar ikon dab'I ta duniya a cikin lambun sana'ar kirkiro hasashen al'adu na Yonghe dake unguwar Dongcheng. Lambun Yonghe, na daya daga cikin wurare na kashi na farko dake tattare da sana'o'in kirkiro hasashen al'adu na birnin Beijing, kuma ya kasance wani sansani ne na bunkasa sana'ar wasan Katun irin na Flash kan yanar gizo na kasar Sin. A kewayen lambun Yonghe, akwai babbar hukumar kula da harkokin labarai da buga littattafai ta kaskar Sin da kuma hukumar kula da harkokin kiyaye ikon dab'I ta kasar da dai sauran wasu hukumomin da abin ya shafa, wadanda suka aza tubali mai inganci ga kafa wani dandamalin yin hidimomi a fannin dab'i.

Mun kuma sami wani labarin cewa, domin karfafa aikin kafa cibiyar musayar ikon dab'I ta duniya, an rigaya an bayyana sunayen shahararrun kwararru guda 10 na kashi na farko a fannin dab'I a matsayin mambobin kwamitin amsa tambayoyi na wannan cibiya, wadanda ko shakka babu za su nuna goyon baya sosai ga aikin raya cibiyar din. (Sani Wang)