Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-13 15:09:43    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (06/02-12/02)

cri

Ran 6 ga wata, a Baku, babban birnin kasar Azerbaijan, shugaban kwamitin wasannin Olimpic na duniya Jacques Rogge ya bayyana cewa, yawan `yan wasan da za a yi musu binciken magani mai sa kuzari a gun gasar wasannin Olimpic ta birnin Beijing zai fi na da a tarihin gasar wasannin Olimpic. A gun taron ganawa da manema labaran da aka yi a wannan rana, Rogge ya bayyana cewa, yawan `yan wasan da za a yi musu binciken magani mai sa kuzari a gun gasar wasannin Olimpic ta birnin Beijing zai kara karuwa daga dubu uku da dari biyar na da zuwa dubu hudu da dari biyar, a sa`i daya kuma, bangaren da abin ya shafa zai kara karfafa aikin tafiyar da magungunan da za a hana yin amfani da su. Rogge ya kara da cewa, dalilin da ya sa haka shi ne domin ana so a yi kokarin shirya gasar wasannin Olimpic ta birnin Beijing mafi tsabta a tarihin gasar wasannin Olimpic.

Ran 6 ga wata, shugaban kwamitin sulhuntawa na gasar wasannin Olimpic ta birnin Beijing na kwamitin wasannin Olimpic na duniya Hein Verbruggen ya yabawa aikin share fage da birnin Beijing ke yi domin shirya gasar wasannin Olimpic ta shekarar 2008 sosai da sosai, shi ma ya bayyana cewa, birnin Beijing zai shirya wata gasar wasannin Olimpic cikin nasara. Verbruggen ya kara da cewa, ana iya ganin sakamakon daga manyan filayen wasannin motsa jikin da birnin Beijing ya gina, alal misali, filin wasan motsa jiki mai siffar `Tafkin Wanka` wato `Water Cube` da filin wasan motsa jiki mai siffar gidan tsuntsaye wato `Bird`s Nest`, ya ce, ya zuwa yanzu, ana gudanar da dukkan ayyukan share fage na gasar wasannin Olimpic ta birnin Beijing kamar yadda ya kamata.

Kwanakin baya ba da dadewa ba, shugaban sashen yin cudanya tsakanin kasa da kasa na kwamitin shirya gasar wasannin Olimpic ta birnin Beijing Zhao Huimin ya fayyace a birnin Beijing cewa, lokacin da ake yin gasar wasannin Olimpic a birnin Beijing, kwamitin shirya wasannin Olimpic na birnin Beijing zai samar da aikin hidima da harsuna hamsin da biyar ga `yan wasa da malaman wasa da jami'ai da za su zo daga kasashe da shiyyoyi dari biyu da biyar. Zhao Huimin ya bayyana cewa, kwamitin shirya gasar wasannin Olimpic ta birnin Beijing zai yi hayar masu aikin fassara na sana'a daga hukumomin gwamnati da jami'an koyon harsunan waje na gida na kasar Sin da kuma kasashen waje, haka kuma za a tabbatar da ingancin aikin hidima a fannin harsuna.

Ran 10 ga wata, an yi zama na 26 na zagaye na karshe na gasar cin kofin kasa ta Afirka ta wasan kwallon kafa a Accara, babban birnin kasar Ghana, kungiyar kasar Masar ta samu zama na farko.(Jamila Zhou)