Kwanakin baya ba da dadewa ba, an yi zama na 11 na gasar wasannin yanayin sanyi ta kasar Sin a birnin Qiqihar da birnin Harbin dake arewacin kasar Sin. Direktan cibiyar kula da wasannin yanayin sanyi ta babbar hukumar kula da wasannin motsa jiki ta kasar Sin ya bayyana cewa, daga ci gaban da aka samu wajen wasan kankara salo-salo, ana iya ganin cewa, tsarin bunkasa wasannin yanayin sanyi cikin dogon lokaci na kasar Sin ya riga ya samu sakamako a bayyane. A cikin shirinmu na yau, bari mu kawo muku bayani kan wannan.
Don kara ingiza yalwatuwar wasannin yanayin sanyi a kasar Sin, babbar hukumar kula da wasannin motsa jiki ta kasar Sin ta tsara wani tsarin musamman wato tsarin bunkasa wasannin yanayin sanyi cikin dogon lokaci, kuma ana fatan za a tabbatar da daidaitawa guda biyu wato 'daidaitawa tsakanin yanayin sanyi da na zafi' da kuma 'daidaitawa tsakanin kankara da kankara mai laushi'.
A da, a sanadiyar yanayi, ana iya gudanar da wasannin yanayin sanyi a wuraren dake arewa maso gabashin kasar Sin inda yanayi ya yi sanyi sosai a yanayin sanyi, amma yanzu, an riga an gina filin kankara a birnin Shanghai da birnin Shenzhen da sauran birane dake kudancin kasar Sin. Saboda sharuddan halittu da za su kawo babban tasiri ga wasannin yanayin sanyi, kuma wasannin yanayin sanyi za su kashe kudi da yawan gaske, shi ya sa kudin da gwamnatin kasa ta gabatar ba zai isa ba, idan ana so a yalwata wasannin kankara, dole ne a nemi kudi daga kasuwanci. Direkta Wang Yitao ya ce: 'Gwamnatin kasar Sin ta nuna goyon baya ga jihohi wadanda ke da shadari da su bunkasa wasannin yanayin sanyi, alal misali, yanzu a hakika dai, kamfanoni sun zuba jari kan yawancin filayen kankara da na kankara mai laushi. Ana iya cewa, daga bunkasuwar wasannin kankara, ana iya ganin bunkasuwar zamantakewar al`umma ta kasa.'
Don sa kaimi ga yankuna daban daban na kasar Sin musamman yankunan dake kudancin kasar Sin da su kara mai da hankali kan wasannin yanayin sanyi, babbar hukumar kula da wasannin motsa jiki ta kasar Sin ta kara wasannin yanayin sanyi guda 14 a gun zama na 10 na gasar wasannin motsa jiki ta duk kasar Sin. Direkta Wang Yitao ya fayyace cewa, a gun zama na 11 na gasar wasannin motsa jiki ta duk kasar Sin, za a sake kara wasannin yanayin sanyi guda 4, ta haka za a kara karfafa wasannin yanayin sanyi a kasar Sin baki daya.
Ban da wannan kuma, kasar Sin tana kara ba da muhimmanci kan wasan kankara mai launi, dalilin da ya sa haka shi ne domin yanzu a kasar Sin matsayin wasan kankara mai laushi bai kai na wasan kankara ba. Kazalika, ana sanya matukar kokari don daga matsayin wasan kankara. Alal misali, wajen wasan kankara salo-salo, ana iya cewa, a gun zama na 11 na gasar wasannin yanayin sanyi ta kasar Sin, matsayin wasan kankara salo-salo ya riga ya dada daguwa bisa babban mataki idan an kwatanta shi da na shekaru 4 da suka shige. Amma cikin dogon lokaci, `yan wasan kankara salo-salo na kasar Sin ba su iya nuna fasaha sosai ba yayin da suke yin wasa, shi ya sa aka bukaci `yan wasa da su mayar da wasa a matsayin nune-nunen fasaha, game da wannan, mataimakin direkta Ren Hongguo ya bayyana cewa, 'A gun gasa, `yan wasan kankara na kasar Sin ba su gwanance kan nune-nune ba, muna fatan malaman koyar da wasan kankara salo-salo za su kara mai da hankali kan wannan.'
A shekarar 2010, za a shirya gasar wasannin Olympic ta yanayin sanyi, daga yanzu, saura shekaru biyu ne kawai, to, ina shirin share fage na `yan wasan kasar Sin? Mr. Ren Hongguo ya fayyace cewa, 'Saboda saura shekaru biyu ne kawai, wato ba lokaci da yawa, shi ya sa kamata ya yi mu kara mai da hankali kan wasanni mafiya muhimmanci da kuma `yan wasa fitattu. Muna fatan za mu samu sakamako mai gamsarwa a gun gasar wasannin Olympic ta yanayin sanyi ta shekarar 2010.` (Jamila Zhou)
|