Bisa sabuwar kididdigar da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayar, an ce, tun daga ran 6 zuwa ran 12 ga wata, wato a lokacin hutu na murnar bikin bazara, yawan kudaden da Sinawa suka kashe domin yin saye-saye ya kai misalin yuan biliyan 255, wanda ya karu da kashi 16 cikin kashi dari bisa makamancin lokaci na shekarar bara.
A lokcin hutu na murnar bikin bazara, an samar da isassun kayayyaki iri daban daban a kasuwar kasar Sin, kuma ba a canza farashinsu ba, a galibi dai Sinawa sun yi saye-saye ba tare da tangarda ba a kasuwar kasar Sin.
Tun bayan kwanaki 10 na tsakiyar watan Janairu na wannan shekara, a sakamakon bala'un matukar sanyi da dusar kankara da kuma matukar bukatar yin saye-saye kafin bikin bazara, farashin kayan lambu da nama da sauran kayayyakin masarufi ya karu kadan a wurare daban daban na kasar Sin. Amma a lokacin hutu na murnar bikin bazara, saboda an samu sassaucin bala'un, an maido da zirga-zirga sannu a hankali, an aiwatar da matakan ba da tabbaci yadda ya kamata, shi ya sa a galibi an sami daidaituwar farashin kayayyakin masarufi, kuma farashin kayan lambu da nama da kwai ya sami raguwa kadan.(Tasallah)
|