Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-12 20:18:31    
Dakin nune-nunen kayayyakin tarihi game da juyin juya hali na babban dutsen Jianggangshan a lardin Jiangxi

cri

Masu karatu, barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin. Ni ce Tasallah da na kan sadu da ku a ko wace ranar Talata.

A babban dutsen Jianggangshan na lardin Jiangxi da ke yankin tsakiya na kasar Sin, ana samun itatuwa masu tarin yawa. Yau fiye da shekaru 80 da suka wuce, 'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin sun kafa sansanin juyin juya hali na kauye na farko a wajen. An mayar da wannan wuri a matsayin wurin da 'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta kaddamar da ayyukan juyin juya hali na kasar Sin. A watan Oktoba na shekarar bara, aka gina dakin nune-nunen kayayyakin tarihi game da juyin juya hali a babban dutsen Jinggangshan a garin Cipi, wanda shi alama ce wajen bayyana tarihin gwagwarmaya da aka yi a babban dutsen Jianggangshan a lokacin da can. Tun bayan da aka bude ta a ran 27 ga watan Oktoba na shekarar bara har zuwa yanzu, mutane na ta kai mata ziyara. Shirye-shiryen da masu zayyana suka tsara wajen nuna kayayyakin tarihi sun sanya mutane su kasance cikin halin da ake ciki a lokacin can. Yanzu bari in jagorance ku, za mu ziyarci wannan dakin nune-nunen tarihi tare domin kara fahimtarmu kan tarihin kasar Sin a lokacin da can.

Bayan da suka shiga karamin zauren dakin nune-nunen, da farko, masu yawon shakatawa sun ga wani mutum-mutumin fitila mai amfani da mai, a bayansa kuma akwai wani babban zane game da babban dutsen Jinggangshan. A yawancin dakunan nune-nunen kayayyakin tarihi na kasar Sin, a kan mayar da mutane a matsayin babban takensu. Amma a dakin nune-nunen kayayyakin tarihi na Jinggangshan, an mayar da fitila mai amfani da mai da kyan karkara na babban dutse a matsayin babban takensa. Game da wannan, Guo Jiasheng, shugaban wani kamfanin wallafa mujalla na lardin Jiangxi ya yi mana bayani cewa, 'Abubuwan da muka gani a karamin zauren wannan dakin nune-nune ya tuna mana da tunanin da aka bi wajen zayyana shi. An tsara shi bisa sabon salo. A da, wannan fitila na kasancewa tamkar fitilar da ke nuna wa masu juyin juya hali na kasar Sin hanyar da za su bi domin samun nasara. Ita ce fitila da Mao Tsedong, wanda shi ne muhimmin shugaban jagorantar juyin juya hali a kasar Sin, ya taba amfani da ita a lokacin aiki. Haskenta ya nuna wa jama'ar Sin makomar aikin juyin juya hali na kasar Sin.'

A cikin wannan dakin nune-nune, ana nuna wa mutane muhimman abubuwan da suka wakana a tarihi. Ana kuma amfani da fasahar zamani domin wasu muhimman al'amuran tarihi, ta haka, maziyarta su kan ji suna kasancewa a lokacin da wadannan muhimman al'amura suka faru.

Kazalika kuma, domin biyan bukatun matasa, dakin nune-nunen ya samar da katun irin na Flash mai ban sha'awa domin karfafa sha'awarsu kan tarihin jan rundunar sojojin kasar Sin.

Abin da kuke saurara a yanzu shi ne wani katun irin na Flash game da yadda rundunar jajayen sojojin kasar Sin ta tsara wata waka game da ka'idojinsu da dokokinsu. Ba safai a kan yi amfani da katun irin Flash a cikin dakunan nune-nunen kayayyakin tarihi ba. Ta hanyar katun, maziyarta, musamman ma 'yan firamare suna iya kara saninsu kan abubuwan da ke cikin wannan waka cikin sauri. Don me ake amfani da katun irin na Flash? Ouyang Suqin, mai kula da ayyukan ginawa na dakin nune-nunen kayayyakin tarihi na babban dutsen Jinggangshan ya gaya mana cewa, 'A karo na farko ne aka yi amfani da katun irin na Flash a dakin ajiye kayayyakin tarihi a kasar Sin. Da farko dai, muna shakkar ko maziyarta za su amince da shi ko a'a. Amma abin gaskiya ya nuna cewa, watakila za a fadakar da matasa yadda ya kamata ta hanyar da suke so.'

Tun bayan budewarsa har zuwa yanzu, dakin nune-nunen kayayyakin tarihi na babban dutsen Jinggangshan ya kan karbi dubban maziyarta a ko wace rana. Dukkan wadanda suka kawo wa wannan dakin nune-nune ziyara sun nuna sha'awa kan kayayyakin tarihi da ake nunawa ta sabbin hanyoyi a wajen. He Hailiang, wanda ya zo daga birnin Changsha na lardin Hunan ya gaya mana cewa, kawo wa wannan dakin nune-nune ziyara ya kyautata halayensa, ya kuma fadakar da shi da tunanin yin gwagwarmaya a ayyuka da zaman rayuwa. Ya ce, 'Ina tsammani cewa, ziyarar irin wannan wuri zai iya kyautata halayena, zai ba da taimako wajen kyautata hadin gwiwa a tsakanin mambobin wata kungiya da kuma inganta yunkurin kungiyar na neman samun nasara.'

To, masu karatu, tare da wannan waka mai dadin ji, bari mu sa aya ga ziyararmu a dakin nune-nunen kayayyakin tarihi na babban dutsen Jinggangshan. Nan gaba, in kun sami dama, ku kawo wa wannan dakin nune-nune ziyara, to, za ku kara saninku kan tarihin rundunar jajayen sojojin kasar Sin yau fiye da shekaru 80 da suka wuce.