Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-12 20:11:53    
gasar rera wakoki da aka shirya a tsakanin daliban kasashen ketare da ke karatu a nan birnin Beijing

cri

Tare da wannan wakar da ke da halin musamman na kabilar Tibet, an soma gasar rera wakoki ta daliban kasashen ketare da ke karatu a nan birnin Beijing ta shekaru 2007.

Mai rera wakar Lim Wen Suen, ta fito ne daga kasar Maysia, yanzu kuma tana karatu a kolejin koyon ilmin kide-kide na kasar Sin. A karkashin tasirin da babanta ya kawo mata, tun lokacin yarantakarta, Lim Wen Suen ta nuna sha'awa da kuma soma koyon kide-kiden al'ummar kasar Sin. Bayan da ta zo kasar Sin, sai ta kara fahimtar kide-kiden al'ummar kasar Sin a dukkan fannoni, ta ce, "Wakokin al'ummar kasar Sin suna da ban sha'awa sosai, a ganina, ya kasance da bambanci a tsakaninsu da na kasashen yamma."

An soma shirya wannan gasar rera wakoki tun daga watan Oktoba na shekarar 2007, daliban kasashen ketare da ke karatu a jami'o'i 36 na birnin Beijing, wadanda yawansu ya kai kusan 200 sun shiga gasar, kuma sun fito ne daga kasashen Korea ta kudu, da Rasha, da Malaysia, da Amurka, da Indonesiya, da dai sauransu.

Bayan da aka yi zabe sau da yawa, 'yan takara 16 sun shiga gasar karshe. A watan da ya wuce, an shirya gasa ta karshe a jami'ar al'umma ta tsakiyar kasar Sin. Halin wakokin da aka rera a gasar na da iri daban daban, ban da wakokin al'umma, kuma akwai wakoki masu karbuwa a ko ina a kasar Sin.

Noh Seung Woo, wani dalibin kasar Korea ta kudu da ke karatu a jami'ar horar da malamai ta birnin Beijing, ya gaya wa wakilinmu cewa, al'adun kasar Sin sun jawo hankalinsa sosai, har ma ya zo nan kasar Sin, domin koyon Sinanci, da kuma al'adun kasar Sin. Ya ce, "Shiga gasar rera wakoki kamar irin, wannan na da amfani sosai kan koyon Sinanci, da kuma fahimtar al'adun kasar Sin."

Mr. He Xiangmin, wani jami'in kolejin ba da ilmi na jami'o'i na birnin Beijing ya gabatar da cewa, yawancin daliban kasashen ketare sun zo kasar Sin ne ba domin koyon Sinanci ba, ko samun ilmin kimiyya kawai ba, lallai sun fi nuna sha'awa kan al'adun kasar Sin. Ta hanyar shirya gasar rera wakoki, ba kawai za a wadatar da zaman rayuwarsu a kasar Sin, da kara fahimta da yin cudanya a tsakaninsu ba, har ma za a horar da su wajen nuna sha'awa kan al'adun kasar Sin.

Francis, dalibin kasar Cameroon, kuma mai jagorar gasar, ya gaya wa wakilinmu cewa, "A ganina, al'adun kasar Sin na da zurfi sosai. A da, na yi tsamani cewa, kasar Sin ta yi daidai kamar sauran kasashe, babu bambanci sosai a tsakaninsu. Amma, yanzu na fahimta cewa, ashe, wannan kasa ce mai wadatuwar al'adu. Yau da shekaru hudu da suka wuce da na zo kasar Sin, na koyi abubuwa da yawa, musamman ma a fannin zaman rayuwa."

Meng Xinyang, shugaban cibiyar kide-kide ta jami'ar al'umma ta tsakiyar kasar Sin, kuma mai tantancewar gasar, ya ce, "Dukkan 'yan takara suna kan babban matsayi, saboda haka, da kyar muka zabi wadanda suka fi kwarewa. Lallai wadannan dalibai sun fahimci al'adun kasar Sin sosai, kuma na yi mamaki kan wannan."

Mr. He Xiangmin, wani jami'in kolejin ba da ilmi na jami'o'i ya bayyana cewa, kolejin nan tana shirya babban aiki a ko wace shekara, don wadatar da zaman rayuwar daliban kasashen ketare da ke karatu a jami'o'in birnin Beijing, a da ya taba shirya gasar rawa, da kwallon tebur, da dai sauransu. Kuma za a cigaba da shirya aikin, don karfafa fahimta da sha'awar da daliban kasashen ketare ke yi kan al'adun kasar Sin.